✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Muhimman batutuwa 10 da Buhari ya tabo a jawabinsa na bankwana

Na ji dadi ganin irin ci gaban da aka samu ta bangaren dawo da kudade masu yawa.

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi jawabinsa na bankwana ga ’yan Najeriya a safiyar wannan Lahadin.

Jawabin nasa na zuwa ne kwana guda kafin ya mika mulkin kasar ga Bola Ahmed Tinubu a ranar Litinin.

Buhari ya yi bayani kan yadda tafiyar mulkinsa ta kasance da kuma wasu matakai da ya dauka a matsayinsa na shugaba.

Ga dai wasu daga cikin abubuwan da shugaban ya yi bayani a kai:

Godiya ga ‘yan Najeriya

Shugaba Buhari ya yi godiya ga jama’ar kasar kan goyon bayan da suka ba shi inda ya bayyana cewa irin kwarin gwiwar da suka ba shi ya taimake shi wurin jagorantar kasar.

Haka kuma shugaban ya yi godiya ga miliyoyin ‘yan kasar wadanda suka yi masa addu’a a lokacin da ya yi rashin lafiya a wa’adinsa na farko.

Taya murna ga Bola Tinubu

Shugaba Muhammadu Buhari ya kara taya murna ga zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu kan nasarar da ya samu ta cin zaben.

“Hakika ka yi aiki tukuru kan wannan rana kuma Allah ya biya maka bukatarka.

“Ba ni da shakka kan girma da kwarewa da adalci da sadaukarwa da nuna daidaito da biyayya da kake da ita ga kasa da kuma son da kake yi yi na Najeriya ta samu ci gaba a idon duniya zai tabbata da ikon Allah, a lokacin da za ka jagoranci kasarmu zuwa matakin da ya fi wanda zan bar ta.

Haka kuma Shugaba Buharin ya bayyana cewa Tinubu ne dan takarar da ya fi cancanta.

Bayar da hakuri kan matakai masu tsauri

A jawabin nasa, Shugaba Muhammadu Buhari ya bai wa ‘yan Najeriya hakuri kan matakan da gwamnatinsa ta dauka masu tsauri amma ya ce matakan sun bayar da sakamako mai kyau.

“A yayin gyara tattalin arziki, mun dauki wasu matakai masu wahala, inda akasarinsu suka bayar da sakamako mai kyau.

Wasu daga cikin matakan sun kawo kunci da wahalhalu na wucin gadi kuma ina bayar da hakuri ga ‘yan kasata,” in ji Shugaba Buhari.

Amma ya bayyana cewa ya dauki matakan ne domin ci gaban kasar baki daya.

Kara inganta dimokuradiyya

Shugaba Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kara inganta dimokuradiyya a kasar domin kuwa zai bar tsarin zabe wanda yake tabbatar da cewa an kirga kuri’u kuma an samu sahihan kuri’u kuma an yi zaben gaskiya da adalci.

Shugaban kuma ya ce tsarin da ya bari ya kara rage tasirin kudi matuka a lokacin zabe wanda hakan zai sa jama’a su zabi wanda suke so.

Buhari ya bayar da misali inda ya ce a zaben da ya gabata an ga wadanda ba su da kudi ko uban gida sun yi nasara kan sauran ‘yan takara masu kudi.

Rage wa talakawa radadi

Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta yi kokari wurin tallafa wa talakawa da mazauna karkara domin samun rayuwa mai kyau.

Ya bayyana cewa gwamnatinsu ta samar da abinci ga miliyoyin mutane da ke kauyuka da kuma bayar da dama ga mata domin su samu abinci.

“Matasa maza da mata da ke birane su ma mun taikama musu domin amfani da baiwarsu yadda ya kamata,” in ji shi.

Nasarori kan harkar tsaro

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi kokari wurin rage wasu daga cikin matsalolin da ake fama da su ne tsaro a kasar.

Buhari ya ce sun samu sakamako mai kyau a yakin da suke yi na ganin cewa ‘yan Nijeriya na zaune lafiya.

“A yayin da nake kammala wa’adina, mun yi kokari wurin rage hare-haren ‘yan fashin da ‘yan ta’adda da fashi da makami da sauran laifuka,” in ji shugaban.

Haka kuma shugaban ya bukaci ‘yan kasar da su ci gaba da ba jami’an tsaro hadin kai domin ganin cewa ba a koma gidan jiya ba.

Kammala ayyuka

A yayin jawabin, shugaban ya tabo batun kokarin da gwamnatinsa ta yi wurin kammala ayyuka musamman ababen more rayuwa.

Shugaban ya ce gwamnatinsa ta kammala ayyukan da aka dade ba a kammala ba kamar wasu daga cikin ayyukan wutar lantarki da gadar Neja ta biyu da amincewa da sake fasali ga dokar man fetur da kammala muhimman hanyoyin da suka hade garuruwa da jihohin Najeriya.

Jimamin wadanda suka rasa rayukansu da wadanda aka sace

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa har yanzu yana jimami kan yaran da ke tsare tare da tabbatar da cewa jami’an tsaro na iyakar kokarinsu domin ceto su.

“Har yanzu ina jimami kan yaranmu da ke tsare, ina ta’aziyya ga iyaye da abokai da ‘yan uwan wadanda suka rasa masoyansu a lokutan da aka rinka kisa na rashin hankali.

Ga duka wadanda ake tsare da su ba bisa ka’ida ba, jami’an tsaro na aiki ba dare ba rana domin ceto su cikin aminci,” in ji shi.

Yaki da cin hanci da rashawa

Shugaban ya ce ‘yan Najeriya suna sane da irin yadda zuciyarsu ke cike da burin ganin ya kawar da cin hanci da rashawa a kasar.

Ya bayyana cewa ya yi ta kokarin wannan yaki duk da irin turjiyar da ake samu.

“Na ji dadi ganin irin ci gaban da aka samu ta bangaren dawo da kudade masu yawa zuwa Najeriya da kuma kwace kadarorin da aka saya da kudaden kasa,” in ji shugaban.

‘Najeriya ta samu ci gaba fiye da 2015’

Batu na karshe da Shugaba Buhari ya yi a jawabin nasa na bankwana shi ne halin da zai bar kasar.

“Ina da yakinin cewa zan bar ofis a 2023 Najeriya ta samu ci gaba fiye da 2015,” in ji shugaban.

A karshe shugaban ya yi godiya ga duka jama’ar kasar da kuma rokon Allah Ya kara wa Najeriya albarka.

%d bloggers like this: