A yau gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf yake cika kwana 100 a kan karagar mulki.
Aminiya ta yi waiwaye kan wasu muhimman ayyuka 10 da ya yi tun bayan karbar mulki daga babbar jam’iyyar adawa ta APC a jihar.
- Kotu ta dakatar da korar da aka yi wa Kwankwaso daga NNPP
- Muna fatan kulla yarjejeniya da ECOWAS — Sojin Nijar:
1. Rusau: Kasa da mako guda bayan kama aiki Gwamnan Abba ya soma cika alkawarin da ya dauka na rusa duk wani gini da aka yi ba bisa ka’ida ba da kuma kwato duk wani wuri na filin gwamnati da aka yi gini ba bisa ka’ida ba.
Wannan lamari ya tayar da kura matuka inda wasu suke goyon bayan hakan wasu kuma suka nuna rashin amincewarsu.
Lamarin ya jawo musayar yawu tsakanin tsoffin gwamnonin jihar ta Kano Rabiu Musa Kwankwaso da kuma Abdullahi Umar Ganduje.
Ganduje ya nuna bacin ransa kan rusau din inda ya ce gwamnatinsa ta bi doka a duk ayyukan da ta yi, inda har ya yi barazanar cewa da zai hadu da Kwankwaso da sai ya sharara masa mari.
2. Biyan albashi 25 ga wata: Tun bayan darewarsa mulki, Abba ya kaddamar da tsarin biyan albashi a ranar 25 ga kowane wata.
3. Biyan kudin jarabawar NECO: Daya daga cikin manufofin gwamnan, shi ne inganta bangaren ilimi a jihar, hakan ya sanya ya biya kudin jarabawar NECO ga daliban makarantun gwamnatin sakandare 55,000 da za su rubuta jarabawar ta 2023.
Ya kuma tabbatar wa al’ummar Kano cewa, gwamnatinsa za ta ci inganta harkar ilimi, wa wanda shi ne ginshikin cigaban kowace al’umma.
4. Rage kudin makaranta: Gwamna Abba ya rage wa dalibai ’yan asalin jihar da ke manyan makarantun jihar kudin makaranta da kashi 50 cikin 100.
5. Biya wa dalibai 7000 kudin makaranta: A baya-bayan nan, Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin biya wa dalibai da ke karatu a Jami’ar Bayero (BUK) kimanin su 7,000 ’yan asalin Jihar kudin makaranta.
Hakan na zuwa ne dai a daidai lokacin da daliban jami’ar ke kokawa da karin kudin da jami’ar ta yi, inda suka rika neman gwamnati da masu hannu da shuni su tallafa musu.
Hatta Jami’ar ta Bayero sai da ta tsawaita lokacin yin rajistar dalibai, kasancewar da dama daga cikinsu ba su iya kammalawa ba, saboda karin da aka yi.
6. Kwato asibitin Hasiya Bayero: A ranar 13 ga watan Agustan 2023 ne, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sake bude asibitin kananan yara mafi tsufa a jihar, wanda gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta rufe.
Bude asibitin shi ne aiki na farko da Abba Gida-Gida ya kaddamar a cikin kwanaki 100 da karbar akalar jagoranci.
Aminiya ta ruwaito cewa, a watan Yuni ne gwamnatinsa ta karbe asibitin da gwamnatin baya ta sayar wa wani mutum a kan kimanin Naira miliyan shida, inda ta kaddamar da gyare-gyare domin a ci gaba da aiki da shi.
7. Dawowar ruwan famfo a Kano: Daga cikin ayyukan farko da sabon gwamnan Kano ya fara kaddamarwa akwai ayyana dokar ta baci kan matsalar karancin ruwan famfo a jihar.
Gwamnan ya bayar da wa’adin mako guda ga Hukumar Ruwa ta Jihar Kano ta gabatar masa bukatunta tare da kawo karshen matsalar ruwan famfo da ake fama da ita a jihar.
Bayan hukumar ta mika bukatunta, gwamnan ya sayi mata sabbin injina da sauran kayan aiki, wanda hakan ya sa ta fara ba ga ruwan famfo a wasu unguwanni da suka shafe shekaru suna sayen ruwan amfanin yau da kullum.
8. Auren zawarawa: Auren zawarawa na daya daga cikin alkawuran da gwamnan ya dauka a lokacin yakin neman zabensa. Bayan ya hau mulki ya ware Naira miliyan 854 ga Hukumar Hisbah ta jihar, karkashin jagoranci Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa don sake aurar da zawarawa.
A baya dai, gwamnatin jihar ta aurar da dubban ’yan mata da zawarawa a karkashin wannan shiri, wanda ake ganin ya samu tagomashi saboda matakai da sharuddan da ake gindayawa kafin yin saki, idan an yi auren.
Gwamnatin tsohon gwamnan Jihar, Rabiu Musa Kwankwaso ne ta fara kaddamar da shirin, wanda ta ce ta bullo da shi ne da nufin rage badala saboda rashin aure.
Sai dai auren zawarawan na wannan karon na shan suka da cece-kuce, inda wasu ke ganin kamar barnatar da kudin jama’ar Kano ne bisa hujjar cewa gara an yi amfani da kudin a wani wajen duba da yanayin kunci da ake ciki a jihar sakamakon cire tallafin man fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi.
9. Fitilun kan titi: Jihar Kano ta shafe shekaru da yin bankwana da hasken fitilar kan titi, amma tun bayan karbar mulki, Abba Kabir Yusuf ya dukufa wajen dawo da haske a wasu titunan jihar.
A yanzu kusan dukkanin manyan titunan kwaryar birnin Kano na rabauta da hasken fitilu da zarar dare ya yi.
10. Rabon kayan tallafi: A ranar Litiin ne Gwamnatin Abba ta kaddamar da rabon kayan tallafi domin rage wa al’ummar jihar radadin cire tallafin man fetur.
Kimanin buhunan abinci masu nauyin kilo goma-goma guda dubu dari 457 wanda ya hada da masara buhu dubu 160 da shinkafa buhu dubu 297 gwamnatin ta tanada don raba wa al’ummar jihar.
Aminiya ta ruwaito cewa kayan tallafin abinci da da aka raba, Gwamnatin Tarayya ce dai ta ba jihohin kasar nan tallafin Naira biliyan biyar biyar don raba wa al’ummarsu a wani mataki na rage radadin janye tallafin man fetur da ta yi.
Gwamnan ya ce tallafin zai fantsama a lungu da sakon jihar kuma kimanin mata 2,357 za su amfana da tallafin awaki da tumaki domin dogaro da kawunansu.
Manoma 1,200 kuma za su amfana da kayayyakin noma da suka har da injinan casa da takin zamani da sauransu.
Sauran wadanda za su amfana da tallafin sun hada da gidajen gajiyayyu da gidajen marayu da nakasassu da makarantun Islamiyya da asibitoci da kananan ma’aikatan gwamnati.