✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Muhimman abubuwan da suka faru a duniyar nishadi ta Najeriya a 2022

A makon nan ne muke bankwana da shekarar 2022, kuma kamar sauran shekarun da suka gabata, abubuwa da dama sun wakana a Najeriya, ciki har…

A makon nan ne muke bankwana da shekarar 2022, kuma kamar sauran shekarun da suka gabata, abubuwa da dama sun wakana a Najeriya, ciki har da masana’antun fina-finai na na Kannywood da Nollywood.

Aminiya ta yi waiwaye domin zakulo wasu muhimman abubuwan da suka faru a masana’antun da suka fi daukar hankalin mutane a wannan shekarar da take nade tabarma.

Dambarawar Nafisa da Sarkin Waka

A watan Janairun 2022 ne aka wayi gari fitacciyar jarumar fina-finan Hausar nan, kuma daya daga cikin manyan jarumar fim din nan mai dogon zango na Labarina, Nafisa Abdullahi ta ce za ta daina fitowa a cikin shirin.

Jarumar ta ce ta yanke shawarar daukar matakin ne saboda ta samu isasshen lokacin gudanar da harkokin kasuwancinta da kuma na karatu.

Nafisa ta tabbatar da hakan ne a cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Instagram, inda ta ce tana mai matukar takaicin yin hakan.

Yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan wannan batun kuma, sai wata muhawarar ta sake barkewa tsakaninsu kan batun tarbiyya, duk da Nazirun ya ce sam ba da jarumar yake ba.

Mutane da dama sun yi ta fashin bakin cewa kalaman Nazirun, wanda ake yi wa lakabi da Sarkin Waka gugar zana ne ga Nafisan.

Sai dai bayan lamarin ya dauki zafi, Naziru ya ce shi ba da Nafisat yake yi a wani sakon murya da ya aika da Aminiya ta samu.

Kalaman da fitaccen mawakin yayi na cewa idan ana neman ’ya’yan da iyayensu suka kasa kula da su a zo masana’antar ta fim ne dai abin da ya kara rura wutar rikici a tsakaninsu.

Sarkin Waka ya wallafa hakan ne a shafinsa ma Instagram da Facebook a wancan lokacin .

Ganduje ya nada Naburaska mai ba shi shawara a bangaren ‘Farfaganda’

A watan Janairun ne dai Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya nada fitaccen jarumin nan na masana’antar Kannywood, Mustapha Naburaska a matsayin mai ba shi shawara kan ‘Farfaganda’.

Jarumin, kuma mai shirya fina-finai a masana’antar, Falalu A. Dorayi ne ya sanar da nadin a shafinsa na Instagram, inda ya taya shi murnar samun matsayin.

Aikewa da Jaruma mai ‘Kayan Mata’ gidan gyaran hali

A  watan Janairun ne dai wata kotun majistare da ke Babban Birnin Tarayya Abuja ta aike da ’yar kasuwar nan da ke sayar da kayan mata, Hauwa Muhammad, wacce aka fi sani da Jaruma, zuwa gidan gyaran hali.

Tun da farko dai ’yan sanda masu shigar da kara sun zargeta ne da yada labaran karya, barazana da kuma bata suna.

Alkalin kotun, Mai Shari’a, Ismaila Abdullahi, ya dage ci gaba da sauraron karar da ba da umarnin a garkameta a gidan gyaran hali na garin Suleja a Jihar Neja.

Tun da farko dai, lauyoyi masu shigar da kara, E. A Inegbenoise da Chinedu Ogada, sun shaida wa kotun cewa wanda yake korafin, Ned Nwoko, ya kai karar Jaruma ta hanyar wani korafi da ta aike a rubuce ga ofishin ’yan sanda na Abuja ranar 20 ga watan Janairu don yin bincike a kai.

Mista Inegbenoise ya ce Jaruma ta yi amfani da kafafen sada zumunta da dama, musamman shafinta na Instagram wajen wallafa bayanan karya a Ned Nwoko da matarsa, Regina.

Ya kuma yi ikirarin cewa Jaruma ta yi amfani da shafin nata na Instagram wajen cewa ta ba Regina Daniels din kwangilar Naira miliyan 10 don ta tallata mata kayan matan.

Lauyan ya kuma ce wacce ake karar ta yi zargin cewa mai kara da matarsa sun karbi kudin nata amma suka ki tallata mata haja, a kwangilar da ba a taba ma kullata ba.

Sai dai wacce ake karar ta musanta laifukan da ake zarginta da aikatawa.

Kannywood ta dauki zafi kan maganar biyan hakkin ’yan wasa

Muhimman labaran 2022 ba za su cika ba, ba tare da an tabo batun nuna yatsa da jiga-jigan masana’antar Kannywood suka yi wa dattijuwa kuma jarumar masana’antar, Ladin Chima ba, kan shaida wa Sashen Hausa na BBC cewa an biya ta N2,000 kudin fitowa a fim.

Mawaki Naziru M. Ahmad, wanda aka fi sani da Sarkin Waka, ne ya fara wallafa wani bidiyo a shafinsa na Instagram, inda ya kalubalanci jarumi Ali Nuhu da Darakta Falalu Dorayi a kan musanta batun biyan Ladin Chima N2,000 da ta ce an yi a matsayin kudin fitowa a fim.

Mawakin ya ce lamarin ba boyayyen abu ba ne, duk wani da ke cikin masana’antar ya san abin da ke faruwa, inda ya bukaci a shafa wa dattijuwar lafiya don ta huta.

Mawakin ya shafe minti 6:45 a cikin wani bidiyo inda ya yi raddi kan maganar Ali Nuhu da Falalu Dorayi kan cewa sun taba daukar kudi N40,000 zuwa sama sun ba wa Ladin Chima.

Sai dai martanin Sarkin Waka bai yi wa wasu dadi ba a masana’antar fim din.

Furodusa Abubakar Bashir Maishadda, ya fito ya caccaki Naziru Sarkin Waka cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram.

“Maganar da Mama Tambaya ta yi a kan cewa ba a taba ba ta kudi sama da N2,000 ko N5,000 wannan ba haka ba ne, zan yi mata uzuri.

“Amma ita ma ta san mutane da yawa sun ba ta sama da wannan kudin a ciki har da ni (Abubakar Bashir Maishadda), akwai Ali Nuhu, akwai Falalu Dorayi da sauransu.

“Mu a Kannywood babu wanda ya taba mana aiki muka hana shi kudinsa, inda akwai wanda muka taba cinye wa kudi ya fito ya fada mana.

“Ka fito kana wasu soki-burutsu a kafafen sada zumunta, kai ba ka isa ka taba mana masana’anta ba mu mayar maka da martani ba, ba ka isa ba.

Ladin Cima ta tayar da kura a masana’atar ne bayan ta bayyana fitowa a shirin ‘Daga Bakin Mai Ita’ tana cewa cewa fim na karshe da ta je ma dubu 2 aka biya ta.

Fitar hirar tata ke da wuya wasu daga cikin masu-fada-a-ji a masana’antar suka fito suna yi mata raddi.

Daga cikin masu yi mata raddi akwai marubuci a masana’antar, Nazir Adam Salihi, wanda ya karyata dattijuwar, inda ya shi da kansa ya taba biyan ta kudade masu kauri.

Nazir wallafa a shafinsa na Facebook cewa, “Na biya Ladi Cima (Tambaya) N4o,000 a fim din Gidan Badamasi Kashi na uku; na sake biyan ta N30,000 a kashi na hudu.

Daga karshe dai bayan shafe kwanaki ana ta cece-kuce kan batun Naziru Sarkin Waka, ya ba wa Ladin Cima kyautar Naira miliyan biyu domin ta ja jari.

Siyasa ta baba kan ’yan Kannywood

’Yan Kannywood sun dade suna bayyana cewa za su shiga siyasa a dama da su domin su samu damar gogayya da masu rike da madafun iko domin su kawo wa masana’antar ci-gaba.

Sai dai a daidai lokacin da zaben 2023 ke kunno kai, an samu baraka a tsakanin masu ruwa da tsaki a masana’antar ta fuskar siyasa.

A 2022 din ne kuma rigima ta balle sosai a tsakanin `yan Kannywood din, har darakta Falalu Dorayi ya wallafa wani dogon rubutu da ya sanya wa suna tsakanin YBN da 13×13, inda a ciki ya ce, “A mahangata, duk kungiyoyin suna aiki ne kusan iri daya: Taimakon mutanen masana’antar da mutanen wajanta. Wannan abu ne da idanu suka gani suka tabbatar.“Shawara ce domin masalaha. Kar ku ba wa shaidan dama wajen shiga tsakaninku, kuma kar ku ba wa zuciya dama ta jefa muku gaba ko kiyayya.

Ita dai 13×13 kungiya ce ta mawaka da ’yan fim da ta hada su Dauda Kahutu Rarara da Adam A. Zango da Aminu Ala da Nura M. Inuwa da Umar M. Shareef da Yakubu Mohammed da Fati Nijar da Aishatu Humaira da sauransu.

A wata sanarwar da suka fitar, sun ce kungiyar ba ta siyasa ba ce, inda suke ce kungiya ce ta taimakon kai-da-kai da taimakon mabukata.

Aminiya ta gano cewa da da fari a cikin kungiyar akwai wadanda suke tallata PDP da wadanda suka tallata APC a zaben wancan lokaci, kafin daga baya ta maida hanakali kan tallata `yan takarar APC a matakin takarar shugaban kasa, ADP kuma a matakin Jiha.

Ita kuwa YBN ta koma tallata APC ne daga sama har kasa.

A 2021 ne dai da aka yi wata ’yar takaddama bayan furodusa Abdul Amart Maikwashewa ya yi taron bikin karrama gwarazan gasar wakar Garkuwan Matasa, wadda mawakan Kannywood suka yi wa Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello, inda aka raba kyautar motoci da babura da sauransu.

Sannan bayan kyaututtukan wakar, Abdul Amart ya raba wa jarumai irin su Bello Mohammed Bello da sauransu.

Shi ma Dauda Kahutu Rarawa ya sa gasar rawa ta wakar Dogara ya dawo, wadda ya rera wa tsohon Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara a lokacin da ya dawo Jam’iyyar APC daga PDP.

An raba kyaututtukan motoci da KEKE-Napep da sauransu ga wadanda suka samu nasara.

Sannan Rarara din ya ba wasu jarumai irin su Tijjani Asase da Jamila Nagudu da Sadiya Sosai da sauransu motoci.

A wani bangaren kuma, Darakta Aminu S. Bono ya wallafa wani dogon rubutu, wanda ya yi na daya da na biyu, inda a ciki ya yaba tare da kawo wasu hanyoyi da dama da mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara ya bi domin kawo sauyi a masana’antar Kannywood.

Kwatsam sai Mansur Make Up wanda na kusa da Adam A. Zango ne sosai ya wallafa cewa, “Rayuwar ’yan fim ta shiga rudani. Wannan ya ce ba don wane ba da harkar ta lalace, wannan ma ya fadi nasa gwanin.”

Sannan ya rubuta cewa, “Kuma babban abin damuwar ita ce in fa ba ka yi hakan ba wai ba ka cikin manya a bangaren da kake yabo, kuma ba su san wannan habaice-habaicen ba ne ya kashe fim din tun farko…”

A kasan rubutun ne darakta, Aminu S. Bono, makusancin Rarara ya rubuta cewa, “Mansur ni ban yi rubutu don ce-ce-ku-ce ba, na yi domin karin karfin gwiwa ga kowane bangare ne saboda ni na san amfaninsu, amma wasu suna amfani da haka don cin mutuncin wasu, ba daidai ba ne wannan.

“Mutane da Allah Ya ba mu suke taimakon masana’antar mu yi musu addu’a tare da fatan samun irinsu da yawa nan gaba, shi ke nan fa rubutuna kuma a ciki na yabi kowane bangare, saboda ko’ina na amfana da su kuma sun amfanar.”

Sai wani mai amfani da sunan Garkwan_Abdulamarta ya mayar wa Aminu S. Bono da martani cewa, “…ka tsargu ke nan?”

Dawowar Maryam Yahaya fim ka’in da na’in

A watan Maris ne kuma fitacciyar jaruma a Masana’antar Kannywood, Maryam Yahaya ta dawo fim bayan ta murmure daga matsananciyan rashin lafiya da ta yi fama da ita.

A shekarar 2021 jarumar ta fara rashin lafiya, inda ta yi matukar ramar da har ya kai ga ba kasafai ake bari ana ganinta ba.

Jarumar a lokacin, ta ce tana fama ne da malariya da typhoid, rashin lafiyar ta sha fama da jinya har ake ganin da wahala ta dawo masana’antar.

A watan Fabrairu kuma, jarumar ta yi tafiya zuwa Dubai domin shakatawa, inda ta rika hotuna da dama, da har wasu daga cikin hotunan suka jawo ce-ce-ku-ce.

Sai dai da samun lafiyarta ta dawo harkar fim, inda a yanzu haka take cikin jaruman fim din Alaqa zango na biyu.

A shekarar 2021 ne dai wani fitaccen mai rubutu a Facebook, Datti Assalafy, ya rubutu a shafinsa, yana kira ga kungiyoyin kare hakkin mata na duniya su kawo wa Maryam Yahaya dauki, inda ya yi zargin cewa abokan sana’arta sun ruguza mata rayuwa, sannan sun mayar da ita wajen iyayenta sun kyamace ta, ko ziyartarta ba sa yi.

Sai dai tun a lokacin masu ruwa da tsaki a harkar suka masa rubdugu, inda suka ce maganarsa zuki-ta-malle ce kawai.

Wanda ya yi wakar ‘Najeriya Jaga-Jaga’ ya kamu da ciwon koda

A watan Yulin 2022 ne  aka yi wa fitaccen mawakin nan da ya yi wakar nan da ta taba yin tashe a shekarun baya ta ‘Najeriya Jaga-jaga’, Eedris Abdulkareem, aikin dashen koda saboda lalurar da daya daga cikin kodojin nasa take fama da ita.

Hakan dai ya bulla ne ta sanarwar da kamfaninsa na Lakeem Entertainment Inc ya fitar.

Sanarwar ta ce tsawon lokaci, an rika yi wa mawakin wankin koda a wani asibiti da ke Jihar Legas, kafin matarsa ta bada ta ta kodar a dasa masa.

“Mamallakin kamfanin Lakeem Entertainment Inc. ya kamu da ciwon koda kuma ya jima ana yi masa wankin kodar a wani asibiti a nan Jihar Legas, Najeriya,” inji sanarwar.

Kuma na masa aikin ne a karshen watan Yuli.

Rasuwar Daraktan shirin Izzar So  

A shekarar 2022 ne kuma Allah Ya yi wa Daraktan shirin Izzar So mai dogon zango, Nura Mustapha Waye, rasuwa.

Lawan Ahmad ne ya sanar da hakan a shafinsa na sada zumunta, inda ya ce, “Inna lillahi wa inna ilaihirrajiuna. Allah Ya karbi rayuwar Nura Mutapha Waye, daraktan fim din Izzar So.”

Marigayin ya dade ana damawa da shi a Masana’antar Kannywood, amma fim din Izzar So din ya daga tauraronsa.

An yi jana’izarsa ne a gidansa da ke unguwar Goron Dutse a Kano.

Watanni kadan bayan rasuwarsa kuma, mai dakinsa ta haifa masa snatalelen da, inda ta mayar masa da sunan margayin wato Nura.

Wani ya maka Hadiza Gabon a kotu kan zargin kin aurensa

A watan Yunin 2022 ne fitacciyar jarumar Kannywood, Hadiza Gabon ta karyata batun mutumin da ya zarge ta da yaudararsa tare da cinye masa kudi Naira dubu 396 da cewa za ta aure shi.

Mutumin ya kai ta kara kotu ne bisa zarginta da cinye masa kudi sannan ta ki auransa.

Lauyan wadda ake karar, Barista Mubarak Sani Jibril ya ce, “Hadiza Gabon ba ta san mutumin ba, kuma ba su taba haduwa ba, ballantana ta masa alkawarin aure.”

Gabon ta bayyana hakan a zaman Kotun Shari’ar da ke Magajin Gari a Kaduna.

Da yake bayani, lauyan mai kara, Barista N. Murtala ya ce wanda yake wakilta din sun hadu da Hadiza Gabon ne a kafar Facebook, inda suka saba har maganar aure ta shiga.

A karshe dai Kotun ta umarci Gabon da mutumin, da su yi sulhu a tsakaninsu.

An tsare wanda ya yi wakar ‘Buga’ a Tanzaniya

A shekarar ce dai ’yan sandan kasar Tanzaniya suka cafke mawakin Najeriyar nan da ya yi wakar nan da take tashe a sassa daban-daban na duniya mai taken Buga, wato Kizz Daniel.

Rahotanni sun ce an kama shi ne saboda ya ki zuwa wajen wani shagali da aka tsara zai rera wakar tasa mai farin jini.

An ce an ga lokacin da ’yan sanda suka cik hannu da shi kuma suka jefa shi a motarsu a babban birnin kasar na Dar-es-Salaam.

Bayanai sun ce an kama Kizz Daniel, wanda asalin sunansa shi ne Oluwatobiloba Daniel Anidugbe, ne saboda saba alkawari, kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu bisa dokokin kasar.

A wani bidiyo na daban da ya karade gari kuma, an ga wasu dandazon masoya da suka biya kudi domin kallon wasan amma burinsu bai cika ba, suna hargitsa filin wasan.

NBC ta haramta sanya wakar Gwanja a kafafen yada labarai

A watan Satumbar 2022 ne hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin ta Najeriya (NBC) ta haramta musu sanya wakar ‘Warr’ ta Ado Gwanja kan zargin lalata tarbiyya.

NBC ta ja hankalin gidajen rediyo da talabijin cewa wakar da shararren mawakin ya yi ta saba Dokar Yada Labarai ta Najeriya saboda tana nuna maye da kuma miyagun kalamai.

Hakan kuwa na zuwa ne a ranar da wasu lauyoyi a Jihar Kano suka yi karar Ado Gwanaja da wasu mawakan Arewacin Najeriya da ke tashe a kafar Tiktok a kotu bisa zargin lalata tarbiyya.

Wadanda aka zayyana a wasikar da aka aika wa Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano sun hada da Ado Gwanja da Sanusi Oscar 442 da Safiya, wadda aka fi sani da Safara’u.

Sauran sun hada Dan Maraya da Amude Booth da Kawu Dan Sarki  da Ado Gwanja, da Murja Kunya, da Ummi Shakira, da Samha Inuwa da kuma Babiyana.

ta ba da misali da cewa baya ga nuna yadda ake yin tangadi a cikin wakar, akwai kalamai na rashin tarbiyya a cikin wasu baitocin wakar.

Alan Waka Da Abbale sun tsaya takara a zaben 2023

A 2022 din ne kuma aka ga ‘yan Kannywood Adam Abdullahi Adam wanda aka fi sani da Daddy Hikima ko kuma Abbale, da fitaccen mawaki, Aminu Ladan Abubakar da aka fi sani da Alan Waka, da kuma Naziru Dan Hajiya suka fito takara.

Duka su uku sun fito takara ne a karkashin jamiyyar ADP, wacce dan majalisar Birnin Kano da Kewaye, Sha’aban Ibrahim Sharada, yake yi wa takarar Gwamna a jihar Kano.

Maganar Safara’u cewa akasarin mata na ajiye bidiyon tsiraicinsu a wayoyinsu

Shekarar 2022, shekara ce da fitacciyar tsohuwar jarumar nan ta shirin Kwana Casa’in, Safeeya Yusuf, wacce aka fi sani da Safara’u  ta dinga tada kura.

Wani batun da tayi da ya hautsina kafafen sada zumunta, shi ne na cewa da tayi kusan duk mata na ajiye bidiyon tsiraicinsu a wayoyinsu.

Safara’u, wacce ke tsokaci a kan wani bidiyonta na tsiraici a shirin Daga Bakin Mai Ita na BBC Hausa, ta ce daga cikin mutanen da take tare da su ne ya yada shi a shafukan sada zumunta.

Jarumar wadda idan ba a manta ba, ta daina fitowa a shirin na Kwana Casa’in bayan bidiyon tsiraicinta ya bayyana a kafofin sadarwa, ta ce tana yin bidiyon tsiraicinta ta ajiye domin nishadi wanda kuma kashi 70 cikin 100 na mata na yi su a ajiye a cikin wayoyinsu.

Wadannan maganganu na ta dai sun tada hazo tsawon lokaci, har a tsakanin jaruman Kannywood.

Batun gina ‘Film Village’ a Kaduna

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da amincewarta da kafa alkaryar fina-finai da aka fi sani da Film Village.

Tuni gwamnatin ta sanya hannu a kan takardar yarjejeniyar gina cubiyar.

An sanya hannun ne a taron bunkasa kasuwanci da tattalin arziki na jihar wato Kaduna Economic and Investment Summit da ake ci gaba da yi a jihar.

Kwamishina kuma Magajin Garin Kaduna, Malam Muhammad Hafiz Bayero, ne ya sanya hannun tare da sauran masu ruwa da tsaki.

Auren Rukayya Dawayya da Afakallah

A watan Nuwambar 2022 ne aka daura auren Shugaban Hukumar Tace Fina-finai na Jihar Kano, Isma’ila Na’Abba Afakallahu, da jarumar Kannywood Rukayya Umar Dawayya.

Tun kafin a soyayyar ta fito fili, jarumar ta rika sanya hotunan Afakallahu a shafinta na Instagram ba tare da nuna soyayyar ba, har zuwa lokacin da Aminiya ta fitar da labarin a  shirinta na Bidiyo mai taken Wata Sabuwa.

An daura daura auren ne a Masallacin Juma’a na Tishama, da ke Kano, sai dai ba a gudanar da shagali kamar yadda aka saba gani a bukuwan Kannywood ba.

Wizkid ba shi da addini

A ranar 6 ga watan Janairun 2022 ne aka wayi gari fitaccen mawakin nan na Kudancin Najeriya mai salon kidan Afrobeats, Ayo Balogun wanda aka fi sani da Wizkid, ya bayyana cewa bai gaskata addini ba.

Wizkid ya bayyana hakan ne cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Snapchat.

A cewarsa, “Ba na tashi daga bacci da wani bacin rai ko damuwa a raina.

“Ba na tashi na tsinci kaina cikin talauci ko tsiya a rayuwa ko a lafiyata da kuma cikin ruhi.

“Ba na tashi da wata kiyayya ko bakin ciki a zuciyata.

“Kada ku bata rayuwarku a kan wani lamari na dan lokaci. Ku yi rayuwa domin kuwa yawan shekaru ba sa ma’aunin dabarar kowane mutum ba.

“Akwai mutane da dama da na sani wadanda sun girma sun tara shekaru amma wawaye ne kuma ba su da wata dabara sannan kuma ni ban yarda da addini ba.”

Dan mawaki Davido mai shekara 3 ya nitse a ruwa

Fitaccen mawakin Najeriya Davido, ya rasa dansa mai shekara uku, mai suna Ifeanyi, sakamakon nutsewa a ruwa.

Bayanai sun nuna Ifeanyi Adeleke ya rasu ne bayan ya nuste a ruwan ninkayar da ke gidan mahaifinsa da ke unguwar Banana Island a Legas, a lokacin Davido da budurwarsa, sun yi tafiya zuwa Ibadan domin halartar wani sha’ani.

Kakakin ’yan sanda na Jihar Legas, Banjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce suna guidanar da bincike.

“An dai gayyaci mutum takwas hadiman gidan Davido din domin amsa tambayoyi, kafin sallamar da dama daga ciki daga baya.

Rasuwar dai ta daki mawakin da masoyiysarsa matuka, wanda hakan ya sa aka wuce da shi gidan mahaifinsa, daga asibitin da gawar yaron take.

An kuma daina jin duriyarsa, har sai a watan Disamba, in da ya gudanar da wasa a Qatar, lokacin gasar Cin Kofin Duniya.

Kazalika hoton da suka dauka tare da masoyiysar ta sa, ya zamo mafi farin jini a tarihin Shafin Instgaram na Najeriya.

An gurfanar da Mawaki 442 a gaban kotun Nijar

A shekarar ce hukumomin jamhuriyar Nijar suka fara shirye-shiryen gurfanar da Mubarak Abdulkarim, wanda aka fi sani da Mista 442 da abokin harkarsa mai suna Mista Ola a gaban kuliya.

Za a gurfanar da mawakan ne bisa zargin mallakar takardun haihuwa na Nijar na bogi.

Alhaji Yusuf Mamman shugaban hukumar gidajen Rediyo da Talbijin na Amfani ne ya tabbatar wa Aminiya hakan a hirar da ta yi da shi, in da ya ce hakika mutanen biyu na tsare tun lokacin da suka shiga hannun jami’an tsaro kimanin makonni biyu da su ka gabata, a inda ake gudanar da binciken kwakwaf a kan su.

Mawakan sun shiga hannu ne a bisa zargin su da mallakar takardun jabu na haihuwar daga Maradi, da kuma kokarin mallakar fasfon kasar domin tafiye-tafiye.

Ya kuma ce, Mawakan sun yi bayyana cewa, wani ne ya yi musu hanyar takardun, da kuma alkawarin samar musu fasfon, jami’an na ci gaba da gudanar da binciken don gano sauran wadanda aka hada bakin da su.

Sun ce da zarar an kamala binciken za a mika su gaban kuliya.

ICPC ta kama mawaki D’Banj

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC), ta ce ta kama fitaccen mawaki Ayo Oyebanjo, wanda aka fi sani da D’Banj  ne bisa zargin damfara da tsarin tallafin Gwamnatin Tarayya na N-Power.

Cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Azuka Ohuhua, ta fitar, ICPC ta ce an kamo mawakin ne domin bincikensa kan badakalar shirin.

Azuka ta ce, “Mun samu korafin yadda wasu ke samun biliyoyin Naira da shirin, bayan wasu da suka rabauta sun ce ba sa samun kudadensu na karshen wata, duk da gwamnati na biya.

“Akalla mutum 10 muka gayyata ofishinmu kan laifukan da ke da alaka da hakan, kuma mun sallami wasu daga ciki.

“Mista Oyebanjo na hannunmu har yanzu, kuma yana shalkwatar ICPC yana taimakawa mana binciken da muke gudanarwa.

“Binciken zai kasance mai fadi, kuma za a mika shi ga sauran masu ruwa da tsaki a yaki da zamba cikin aminci, da kuma bankunan da wadanda suka ci gajiya suka bude asusu.

Sai dai daga baya ICPC din ta saki D`banj bayan yi masa tambayoyi.