✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Muhimman abubuwa 8 da suka faru a Kannywood cikin makon jiya

Ga wasu muhimman abubuwa 8 da suka faru a makon nan a masana’antar Kannywood.

Adam A. Zango ya sanya wa ’yarsa sunan mahaifiyarsa

Fitaccen jarumi a masana’antar Kannywood, Adam A. Zango ya sanya wa ’yarsa sunan mahaifiyarsa.

Jarumin ne ya bayyana hakan a shafinsa na Instagram, inda ya ce, “Godiya ta tabbata ga Allah S.W.T! Allah Ya raya mana ita bisa turbar addinin Musulunci.

“Allah Ya shirye ta Ya sa Annabi Muhammad S.A.W ya yi alfahari da ita ranar lahira! Sunanta Furaira Adam. Sunan mahaifiyata ne. Amma sunan kunyarta Princess Diyanah.

– Ali Nuhu bai taya Zango murnar samun karuwa ba

Sai dai kamar al’ada take a Kannywood, idan wani abu ya samu wani jarumi, jaruman masana’antar sukan sanya hotuna ko su yi rubutu su sanya a shafukansu na Instagram su taya shi murna ko jaje.

Sai dai Aminiya ta garzaya shafin Ali Nuhu, inda ta duba daga mako biyu da suka gabata zuwa yanzu, amma babu inda jarumin ya taya Adam Zango murnar samun karuwar haihuwar.

– Avengers: Fim din Ingilishi na Hausawa

An shirya tsaf domin fara haska fim din Avengers, wanda na Ingilishi ne na Kannywood a sinimomin Jihar Kano.

Daga cikin jaruman fim din akwai Ali Nuhu da Tijjani Asase da Zulaihat Zee Pretty da sauransu.

Ibrahim Birniwa ne ya tsara labarin, M. M. Haruna ya fassara, Nazifi Asnanic da Usman Mu’azu suka shirya, M. M. Haruna ya dauki nauyi, sannan Bature Zambuk ya bayar da umarni.

– Kamar ba mu da Shugaban Kasa a Najeriya — Mansurah Isah

Tsohuwar jarumar Kannywood, Mansurah Isah, ta koka kan yadda a cewarta kowa yake yin abu yadda yake so a Najeriya.

A wani bidiyo da ta saka, wanda Aminiya ta gani, an jiyo ta tana cewa, “Wannan wahalar man fetur din na san akwai man a gidajen man da ake ta rufewa. Kawai suna rufewa ne domin talaka ya sha wahala. Da wanne za mu ji?”

Sannan ta rubuta cewa, “Don Allah ku taimaka. Tura ta kai bango. Kamar ba mu da shugaba a kasa. Kowa yana abin da ya gadama. Talaka sai wahala kawai yake sha. In ka yi magana a ce Dala ta tashi. Yaya za mu yi?”

– An ba Furodusa Uzee Usman Digirin Digirgir a Togo

Wata jami’a a kasar Togo ta karrama Furodusa a Kannywood, Uzee Usman da Digirin Digirgir.

Darakta Falalu Dorayi ya sanya hotonsa, sannan ya ce, “Ina taya ka murna, Uzee Usman bisa samun karramawa ta Digirin Digirgir daga Jami’ar Iheris da ke Togo.”

Uzee Usman rike da karramawar Hoto: Instagram na Falalu Dorayi

– Nafisat Abdullahi ta bude shagon kwalliya

Jaruma Nafisat Abdullahi ta bude shagon kwalliya a Jihar Kaduna.

Sunan shagon Naf Cosmetics.

– Jaruman Kannywood da suka tafi Umarah

Daga cikin jaruman Kannyood da suka tafi Umara akwai tsohon Furodusa AS Mai Kwai da Abdul Amart Mai Kwashewa da Aisha Izzar So da Sadiq Sani Sadiq.

Sadiq Sani Sadiq da Aisha Izzar So da Abdul Amart a Umarah. Hoto: Instagram na Aisha Izzar So.

– Almajirai sun je kallon fim din Fanan

Mansurah Isah wadda ita ce ta dauki nauyin fim din ne ta bayyana hakan, inda ta sanya hotonta tare da almajiran, sannan ta ce, “Ga ni a tare da almajirai 40 da Hadiza Gabon ta dauki nauyinsu su zo su kalli fim din Fanan a sinimar Platinun da ke hanyar Zaria a Kano.

“Sun ji dadi sosai, kuma ni ma na yi farin ciki. Allah Ya faranta miki ke ma.”

%d bloggers like this: