Murabus din Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya kawo karshen tirka-tirkar da aka samu a cikin jam’iyyar bayan shugabanni biyar da ta taba yi tun kafa ta a 2014.
Tsohon Gwamnan Jihar Osun, Bisi Akande shi ne shugaban ta na farko sannan sai John Odigie Oyegun sai Adams Oshiomhole da gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe, a matsayin riƙon ƙwarya kafin a zaɓi Adamu.
Za a iya cewa yawancin shugabannin da aka yi, ba a kwashewa lafiya. Haka shi ma da aka zo kan Adamu ba rabu ta daɗi ba, bayan ɗauki ba daɗi da aka yi ta fama da shi.
Mun zaƙulo muku wasu ka-ce-na-ce da kai ruwa rana da aka yi ta yi a lokacin shugabancin Adamu, wanda aka zaɓe shin a ranar 26 ga watan Maris na shekarar 2022, kimanin shekara ɗaya da rabi ke nan yanzu.
Cacar baki tsakaninsa da Salihu Lukman
Ana ganin cewa an samu musayar zafafan kalamai tsakanin tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa da mataimakin sa a Arewa maso Yamma, Malam Salihu Lukman, wanda shi ma ya shigar da wata ƙara domin a tsige shi.
Da ƙyar Adamu ya sha a lokacin da Lukman ya rubuta masa wata wasiƙa yana sukar yadda yake tafiyar da harkokin jam’iyyar.
A wata wasika mai ɗauke da kwanan watan 27 ga watan Mayu, 2022 da ya aike wa Adamu kafin gudanar da babban taron jam’iyyar na zaben dan takarar shugaban kasa, Lukman ya ce yadda tsohon Shugaban na gudanar da lamuran jam’iyar sun saɓa ƙa’ida.
Haka ma Lukman, ya sake rubuta wata wasika a watan Afrilun 2023, yana zargin Adamu da Sakataren jam’iyyar Iyiola Omisore da gudanar da shugabancin jam’iyyar a tsari na ƙarfa-ƙarfa.
Ya kuma yi zargin ana facaka da kudaden jam’iyyar ba tare da bin ƙa’ida ba. Lamarin ya sa har lokacin da Adamu ya ajiye shugabancin ba sa ga maciji tsakaninsa da Lukman.
Daukar bangare a zaben fid-da gwani
Ana dab da gudanar da zaben fid-da gwanin ɗan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, wanda shugaba mai ci, Bola Ahmed Tinubu ya lashe, Adamu ya fito ƙarara ya bayyana cewa cewa jam’iyya na goyon bayan Shugaban Majalisar Dattawa na wancan lokacin, Sanata Ahmad Lawan, kuma a matsayin ɗan takara na sulhu wanda tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da shi.
Sai dai ba a kwashe ta dadi ba bayan sanarwar, inda da dama daga cikin ’ya’yan jam’iyyar suka nuna bara’a da matakin musamman Shugaba Bola Tinubu wanda a lokacin ake hasashen shi ne zai lashe zabe ba tare da wata tantama ba.
Rashin tabuka abin kirki a zabukan gama-gari
Tsohon Shugaban na APC ya gaza kawo rumfar sa a zaɓukan da aka gudanar na Shugaban Kasa, duk da yake yana matsayin shugaban jam’iyya na kasa da ake kallo a matsayin jigo, inda har a mazaɓarsa ya sha kaye kuma Tinubun bai ci jiharsa ta Nassarawa ba.
Adamu wanda ya kaɗa ƙuri’arsa a mazaɓar Angwarimi, GRA, a akwati mai lamba A1-PB da ke Keffi a Jihar Nasarawa, ya sha kaye hannun jam’iyyar LP, inda Peter Obi ya samu ƙuri’u 132, yayin da Tinubu ya zo na biyu da ƙuri’u 85.
Da yawa daga cikin ’yan APC dai sun yi ta ce-ce-ku-ce inda suke ganin hakan wata alama ce da ke nuna bai yi wa Tinubu kamfe ba, idan har zai iya rasa rumfarsa, sakamakon ƙarfin ikon da yake da shi a matsayin tsohon gwamna kuma sanata bugu da ƙari shugaban jam’iyya na ƙasa. Ya kuma kasa cin zaɓen Gwamna a jihar.
Rikicin cikin gida
A lokacin tsohon shugaban APCn, an yi ta samun rikice-rikice na cikin gida a jihohi da dama, amma ya kasa shawo kansu. Daya daga cikin jihohin da suka yi fama da rikici sosai ita ce jihar Kwara inda dukkanin shugabannin jam’iyyar ke musayar kalamai. An kuma samu rabuwar kawuna a gidan jam’iyar APC na Kwara ta yadda kowa sai da ransa ya ɓaci, kuma wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyar suka fusta matuƙa.
Baya ga jihar Kwara, akwai wasu jihohin da rikici ya dabaibaye su, tun daga batun zaben shugabanni a matakin mazaɓa da Kananan Hukumomi, da suka haɗa da Legas, Osun, Bayelsa, Ribas da Kano da dai sauransu.
Tawaye da sunayen shugabannin majalisa
Bayan ayyana manyan jagororin Majalisar Dokokin ta Kasar suka hada da Shugaban Majalisar Dattawa, Shugaban Majalisar Wakilai, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa da Mataimakin Shugaban Majalisar, Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio da Kakakin Majalisar Tajudeen Abbas ne suka bayyana sunayen sauran shugabannin majalisun biyu.
Sai dai, Sanata Abdullahi Adamu ya yi ɓaɓatu game da cikon shugabannin da aka sanar na majalissun dokokin kasar, inda ya nuna rashin gamsuwa da zaɓen da aka yi na masu rinjaye da mai tsawatarwa da wadansu mukaman wadanda ya ce ba a tuntuɓe su ba kafin yanke shawara.
Da yawa daga cikin shugabanni da jiga-jigan jam’iyyar na ganin ficewar shugaban jam’iyyar a matsayin nuna bara’a da shugaban ƙasa da ake ganin ya amince da jerin sunayen.
Wani jigo a jam’iyyar APC kuma tsohon sakataren yada labaran jam’iyyar a jihar Legas, Joe Igbokwe ya ce wa’adin Adamu a matsayin shugaban jam’iyyar ya ƙare, don haka a bar shi ya koma gefe.
Rashin halartar taron Gwamnonin 1999 da Tinubu
Ana zargin tsohon shugaban jam’iyyar da ƙin halartar ganawar tsoffin Gwamnoni da suka yi mulki a shekarar 1999 tare da Shugaban Kasa.
Adamu na ɗaya daga cikin rukunin gwamnonin, amma duk da yake yana matsayin shugaban jam’iyya wanda ake sa ran ya tarbi takwarorin nasa, amma ya yi biris da ganawar, wadda tsoffin Gwamnoni kusan 19 suka halarta.
Masu sharhi na ganin hakan ya ƙara bayyana tsamin dangantaka da ke tsakaninsa da Shugaban Kasa wanda ake kallo a matsayin uban jam’iyya.
Tsokaci a kan lafiyar Gwamnan Ondo, Akeredolu
Duk da yake ta iya yiwuwa ya yi hakan da kyakkyawar niyya, amma ana ganin kalaman Adamu akan ƙoshin lafiyar Gwamnan Ondo Oluwarotimi Akeredolu a makon da ya gabata ya fusata da damad aga cikin ‘ya’yan jam’iyar. Akeredolu yanzu haka dai yana samun kulawar likitoci a kasashen ketare.
A wani taro da aka yi da shugabannin APC na jihohin ƙasar, Adamu ya ce Akeredolu, “yana cikin mawuyacin halin da ba zai iya shugabanci ba”, inda ya tafi hutun kwanaki 21 tun a ranar 7 ga watan Yunin 2023, ana sa ran ya dawo a ranar 6 ga watana Yuli, amma ya ƙara wa’adin nemo lafiyar ta sa.
Ko da yake, Adamu ya yi masa addu’ar samun sauƙi cikin gaggawa.
Saidai jim kadan bayan Adamu ya yi magana a wajen taron, Gwamnan Jihar Ondo ya fitar da wata sanarwa da kakkausar murya a kansa, inda ya ce sabanin maganar da ya yi, gwamnan bai gaza ba kuma a halin yanzu yana samun sauki.