✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muhammad Abacha ya zama dan takarar Gwamnan PDP a Kano

Ya samu nasarar ce bayan lashe zaben fid da gwanin jam’iyyar

Muhammad Abacha, da ga marigayi tsohon Shugaban Najeriya na mulkin soja, wato Janar Sani Abacha, ya samu nasarar zama dan takarar Gwamnan Kano a jam’iyar PDP a zaben 2023.

Baturiyar zaben, Amina Garba ta ce ya samu nasarar ne ranar Laraba da kuria 736 a zaben fid da gwani na jam’iyyar.

Shugaban kwamitin zaben jam’iyyar, Alhaji Muhammad Jamu ya ce zaben an yi shi ne ta halastacciyar hanya da ingantattun daliget, da kuma sahalewar hukumar zabe, jami’an ’yan sanda, da rundunar tsaro ta farin kaya.

An gudanar da zaben ne ranar Laraba a Kano, kamar yadda uwar jam’iyyar ta tsara.

A shekarar 2011, Muhammad Abacha ya tsaya wa tsohuwar jam’iyyar CPC takarar kujerar, hakama a 2019 ya tsaya a jam’iyyar APDA, sai dai ya yi rashin nasara a duka zabukan.