Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Mufti Menk, ya taya kasar Argentina da fitaccen dan wasanta, Lionel Messi murnar lashe Kofin Duniya da aka yi a kasar Qatar.
Malamin ya taya murnar ce a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter da yammacin Lahadi, jim kadan bayan kasar ta doke Faransa a wasan karshe ta hanyar bugun fanareti.
- DSS ta janye dakarunta daga gadin Gwamnan Osun
- NAJERIYA A YAU: Asarar Da Najeriya Ta Yi Saboda Rashin Zuwa Gasar Kofin Duniya
Malamin ya wallafa a shafinsa nasa cewa, “Sannu da kokari Qatar, sannu da kokari Messi, sannu da kokari Mbappe, sannu da kokari Argentina! Ina taya ku murna.”
Well done #Qatar
Well done #Messi
Well done #Mbappe
Well done #Argentina
In that order!
Congrats!— Mufti Menk (@muftimenk) December 18, 2022
Sai dai jim kadan da wallafa sakon, masu amfani da shafin na Twitter sun shiga bayyana ra’ayinsu a karkashin wallafar malamin, inda wasu suka bi sahu wajen taya su murnar, wasu kuma na kalubalantar yadda yake tsokaci a kan harkar ta kwallon kafa, a matsayinsa na malami.
Wani mai suna MD Mahadi Hassan, ya ce, “A maimakon haka, zai fi kyau ka rika rubuta mana ayar Alkur’ani da za ta taimaka mana mu fahimci duniya.”
Shi kuwa wani mai suna Dolski cewa ya yi, “Ya kamata [Mufti] Menk ya zama gwarzon wannan gasar tarin basirarsa. A ina ake samu irin wannan mutanen?”
Shavi Sharif kuwa tambaya ya yi yana cewa “Yaushe Mufti ya koma mai goyon bayan kwallon kafa kuma?”
A cewar Abubakar Salmanu Muhd kuwa ya ce, “Assheikh kai ma kana shakatawa ke nan, Allah Ya baka Aljannar Firdausi da kai da dukkan al’ummar Musulmai. Muhd Salmanu daga Kano Najeriya.”
Kazalika, wasu kuma sun kalubalance shi kan yadda suka ce kasar ta Qatar ta bar maza da mata sun cakuda yayin kallon wasan amma malamin bai ce komai ba, duk da yake ta hana tallan giya a fili da kuma hana masu auren jinsi daya.