A yayin da muka karkare ibadar azumin Ramadan, muna rokon Allah Ya sa mun dace da wadanda aka gafarta mawa. Ga shi kuma mun yi ban kwana da gwaggwabar lagwadar da ake samu a Ramadan, wacce Allah (SWA) Ya alkawarta mana, Ya sanar da mu ta hannun manzonSa Muhammadu (SAW). Muna rokon Allah Ya nuna mana Ramadan na gaba da ma na badin-badin-badada.
A yayin da muka samu dacewa da yin ibadar Ramadan cikin dadi da walwala, wasu daga cikin ’yan uwanmu a kasar nan da sauran sassan duniya, ba su samu tagomashi irin namu ba, domin kuwa sun kasance cikin jarabawar matsaloli daban-daban. A nan sai dai mu ce inna lillahi wa inna ilaihi raji’un (Daga Allah mu ke kuma gare Shi makoma take).
Jihar Borno, Najeriya:
A jihohin Borno da Yobe, al’ummarmu sun kasance cikin tashin hankali, sun kasance cikin jarabawar ibtila’in kashe-kashe da asarar dukiya. Yaransu ma har sun saba da jin karar bindigogi, ga shi sun kasance cikin takunkumin zaman gida, ga kuma rashin kafar sadarwa, duk da cewa an dan sassauta ta. A haka suka yi azuminsu cikin jarabawa da wahala. Muna rokon Allah Ya kawo dauki, al’amarinsu ya samu sawaba.
’Yan uwa Musulmi na Masar:
A Masar, an shiga hatsaniya da rudani da tashin hankali, an kauce wa hankali da tunani. Jam’iyyar ’Yan uwa Musulmi (ko Masu Tsattsauran Ra’ayin Musulunci, kamar yadda Turawan Yamma ke son kiransu), sun tashi tsaye wai suna zanga-zangar neman dimokradiyya. A yayin da shi kuma dan barandan kasashen Yamma, Mohamed el Baradei ya dare kan mulki, a cikin gwamnatin da ta yi hannun riga da dimokradiyya, gwamnatin soja. Al’amura sai kara canzawa suke ga al’amuran da duk aka ce na Musulunci ne! Miliyoyin ’yan uwa Musulmi da iyalansu sun fantsama zuwa Masallacin Madinat Nasr Rabia da ke Kairo. Babu abin da suke kiran a yi sai a dawo da halastaccen shugaban da suka zaba a dimokradiyyance, Mohamed Morsi. Sama da wata daya, aikin da suke ke nan, a nan suke azuminsu, nan suke sahur da buda-baki, kamar kuma yadda a nan suke dukkan sallolinsu. Sojoji sun kashe da dama daga cikinsu, amma duk da haka sun jajirce bisa manufarsu. (Yanzu dauki misalin a ce makamai suka dauka suka ce za su kare ‘dimokradiyya,’ da wane suna kake jin Turawan Yamma za su kira su? ‘Yan ta’adda! Shin a irin wannan rashin adalci, wane mataki ’yan rajin kare hakkin dan Adam suke yi? Kallo kawai!)
Al’ummar Musilmin Aighur, dinjiang, China:
Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Al’ummar Musulmin Aighur suna cikin matsala, domin kuwa hukuma ta kafa musu tsattsaurar dokar haramta musu gabatar da ibadar azumi. Hukumar kasar ta hana su sakat, domin kuwa ita dama babu ruwanta da addini, duk kuwa da cewa akwai Kiristoci kuma tsiraru amma ba a tsangwamarsu kamar yadda ake wa al’ummar Musulmin wurin. An tilasta wa Musulmi ma’aikata dole su aje azumi. Da rana kata za a ba su abinci, kuma dole su ci, idan ba haka ba, mutum ya yi laifi ke nan, kuma dole a hukunta shi, ko dai a kore shi daga aiki ko kuma a hana shi ijararsa. Haka ake bi ana ta cin zarafinsu, hatta yaran makaranta ba a bari ba. Duk dalibin da aka ba abinci da rana ya ki ci, aka gano yana azumi, to ya gamu da bala’i ke nan. (Da irin wannan kaskanci da ake wa al’umma, idan ka tambayi cewa wane mataki masu kare hakkin dan Adam suke dauka? Kallo kawai!)
Al’ummar Musulmin Rohingya na Myanmar (Burma):
Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Labaru ta kafofin intanet sun karade ko’ina, cewa al’ummar Musulmin Myanmar suna cikin ukuba. A yayin da la’antattun ’yan kwaminisanci ke gasa wa al’ummar Musulmin China ukuba, su kuwa na Myanmar, mabiya addini Buddha ne ke uzura musu. ’Yan Buddha, da suke ikirarin zaman lafiya da son lumana, amma suke irin wannan cin mutunci! Kamar yadda labari ya tabbatar, ’yan Buddha suna ta kashe Musulmi, suna yi wa matansu fyade. Sun hana su gudanar da Sallah, ko masalacci ma ba a bari a gina. Hakka Sallar jana’iza ma, sai dai a boye suke gudanar da ita, idan wani nasu ya mutu. Irin wannan wariyar addini da kaskanci, abin da al’ummar Musulmin wurin ke fuskanta ke nan a kullum. (A misali a ce wadannan al’umma su dauki makamai, su ce za su kare kansu, da wane suna Turawan Yamma za su kira su? ’Yan Ta’adda! Kuma shin wane makaki ’yan kare hakkin dan Adam suke dauka kan haka? Kallo kawai!)
Sansanin ’Yan Gudun Hijira na Zaatari, a Syriya:
A Syriya, alkaba’in kashe-kashen rayuka da aasarar dukiyoyi sun yawaita, wanda haka ya sa al’umma suke ta yin gudun hijira zuwa sansanin Zaatari da ke makwabtaka da birnin Jordan. Akwai sama da mutum miliyan daya a wannan sansani, maza da mata, yara da manya. An raba su da gidajensu da dukiyarsu da kwanciyar hanklainsu. A nan sansanin suke azumi, suke buda baki, suke sahur da sallolinsu.
Bida, Najeriya:
Gare ki sabuwar ’yar uwarmu a Musulunci, A’isha Uzoechina tare kuma da dubban wadanda suka amshi Musulunci bisa zabin kansu, kafin da bayan Ramadan; wadanda kuma suka gabatar da ibadar azumi cikin wahala da tsangwama, muna yi muku addu’a, Allah Ya ba ku kariya. Barka Da Sallah!
Mu tuna da ’yan uwanmu da ke cikin wahala
A yayin da muka karkare ibadar azumin Ramadan, muna rokon Allah Ya sa mun dace da wadanda aka gafarta mawa. Ga shi kuma mun yi…