✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mu Sha Dariya: Ibo da kudi

Kai wane irin mutum ne, ta mota kake alhali ba ka lura ba cewa an datse maka hannu ba.

Wani Ibo ne ya yi hadari da sabuwar motarsa mai tsada, ya yi kokari ya tashi ya kira dan sanda ta waya.

Da ya iso wurin sai ya ce masa: “Don Allah ka duba ka gani, wannan mai motar ne kawai ya zo ya buga wa sabuwar motata mai tsada, ga shi duk ta lalace.”

Dan sanda ya girgiza kansa, ya ce wa Ibo: “Kai wane irin mutum ne, ta mota kake alhali ba ka lura ba cewa an datse maka hannu ba, ga shi nan yana ta zubar jini?”

Ibon nan ya duba ya ga babu hannunsa daya, sai ya saka kuka, ya ce: “Chineke, ina agogona da zobbana na zinare!?”

Daga Bashir Yahuza Malumfashi, 08065576011