✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mu sha dariya: Haska min in dau takalmina!

Labarin fada tsakanin Basakkwace da wani dan zamani

Wani Basakkwace ne fada ya hada su da wani matashi dan zamani.

Basakkwace, ya ja baya ya yi tsayuwa irin ta ’yan dambe shi kuma matashin ya yi tsayuwa irin ta ’yan damben zamani.

Suna haduwa, da Basakkwace da ya ji duka ya yi masa yawa, sai ya ce da abokinsa, “Almu wai cikin masu buguna ba ka rika min guda!”

Sai Almu ya ce, “Ai mutum guda ka bugunka!”

Sai Basakkwace ya ce, “Yanzu wannan bugu, bugun mutum guda na?”

Almu ya ce, “Awo shi na!”

Basakkwace ya ce,  “To haska min in dau takalmina!”

Almu ya ce “Ho aiki ya baci, ai rana ce ba dare ba!”

Labari daga 07086866165