✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mu Sha Dariya: Gasar addu’a

Ya Allah! Duk abin da ka ba Banufen nan, ka ba ni irinsa ninki biyu.

Zauren Mu Sha Dariya na Aminiya ya kawo muku wani labari yadda ta kaya tsakanin wani Banufe da wani mutumin Hadejia da suka hadu a bakin Ka’aba a Saudiyya. 

Wani Banufe ne yake ta rokon Allah a Dakin Ka’aba, sai wani Bahadeje da ke kusa da shi, ya daga hannu yana rokon Allah yana cewa: “Ya Allah! Duk abin da ka ba Banufen nan, ka ba ni irinsa ninki biyu.”

Ko da Banufen nan ya ji haka, sai ya ce: “Ya Allah Ka sa idona daya ya nakasa.”

Ke nan idan ido daya na Banufe ya mutu, shi Bahadeje zai rasa nasa idanun biyu.

Daga Kabir Sakaina Layin ’Yangoro Malumfashi