Fitaccen Malamin Addinin Musuluncin nan, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya zayyana wasu muhimman abubuwan da ya kamata mai azumi ya lazimta a watan Ramadan.
Yayin da al’ummar Musulmi ke gudanar da ibadar azumi, Sheikh Daurawa ya bayyana cewa akwai ɗimbin lada ga duk wanda ya aiwatar da waɗannan ayyuka:
1. Azumi: Mai azumi ya kula da azuminsa, ya san hukunce-hukuncensa, ya kiyaye su, tare da nisantar abin da zai rage lada ko karya azumi.
2. Sallah: Ya fi dacewa a dage da Sallar Taraweeh da Tahajjud, tare da yin sallolin farilla a cikin jam’i da nafiloli da ake yi kafin ko bayan su.
3. Ciyarwa: Ciyarwa tana da matuƙar muhimmanci, ko da dabino ko ruwan sanyi ne. “Domin Annabi (SAW) ya ce, duk wanda ya ciyar da mai azumi, za a ƙara masa lada kamar ya yi wani azumin ne,” in ji Sheikh Daurawa.
4. Umrah: Idan mutum yana da hali, yana da lada mai girma yin Umrah a watan Ramadan. Idan kuwa ba shi da hali, sai ya maye gurbinsa da ciyarwa.
5. I’tiƙafi: Sheikh Daurawa ya shawarci Musulmi da su mayar da hankali wajen shiga I’tiƙafi, idan suna da hali, domin yin ibada tare da nesantar shagalin duniya.
6. Daren Lailatul Ƙadar: Ya buƙaci Musulmi da su dage da neman dacewa da daren Lailatul Ƙadar ta hanyar yin salloli, addu’o’i, da sauran ayyukan alheri.
7. Yafiya: Sheikh Daurawa ya buƙaci Musulmi da su yafe wa juna, domin neman gafarar Allah a cikin wannan wata mai alfarma.
8. Karatun Al-Ƙur’ani: Ya ce ya dace Musulmi su dage da yawaita karatun Al-Ƙur’ani, domin a watan Ramadan aka saukar da shi.
9. Addu’a: Yana da muhimmanci a dage da yin addu’a, musamman a lokacin Sahur, lokacin buɗa-baki, da lokacin da ake cikin azumi, domin a waɗannan lokuta Allah na karɓar addu’o’i.
10. Zumunci: Sada zumunta a watan Ramadan yana ƙara albarka, arziƙi, da zaman lafiya, kamar yadda Sheikh Daurawa ya bayyana.
11. Tausayi: Azumi yana koyar da tausayi da taimako, domin mai azumi zai jin halin da masu buƙata ke ciki, hakan zai sa ya fi jin ƙansu.