Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, ta musanta raɗe-raɗin shirya addu’ar ƙasa domin magance mawuyacin hali da ’yan Najeriya ke ciki.
Wasu rahotanni sun bayyana cewar Uwargidan Shugaban Ƙasa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro, Malam Nuhu Ribadu, na shirin gudanar da addu’a ta tsawon kwana bakwai.
- Tinubu zai halarci taron ƙasashen Larabawa da Musulunci a Saudiyya
- Mutum 20 sun tsere daga Cibiyar Horar da Nakasassu ta Abuja
Shirin na da nufin neman sauƙi daga Ubangiji kan halin da ƙasar ke ciki.
An ruwaito cewar za a haɗa addu’ar ne tare da jagororin addini daga ɓangarorin Kirista da Musulmi.
Sai dai, mai magana da yawun Uwargidan Shugaban Ƙasa, Busola Kukoyi, ta musanta hakan cikin wata sanarwa a ranar Asabar.
Ta bayyana cewa, “Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ba ta hannu wajen shirya wata addu’ar ƙasa ba.
“Labaran da ke yawo a kafafen yaɗa labarai da na sada zumunta ba gaskiya ba ne kuma suna ƙunshe da yaudara. Mutane su yi watsi da wannan labari domin ba gaskiya ba ne.”
Kukoyi ta ƙara da cewa, duk da cewa Uwargidan Shugaban Ƙasa, a matsayinta na Kirista, tana goyon bayan yin addu’a kuma tana ganin ya dace a yi wa Najeriya addu’a.
Sai dai ta ce wannan hakki ne na lowane ɗan Najeriya, addini, ƙabila ba tare da nuna bambancin siyasa ba.
Ta kuma shawarci jama’a da su tabbatar da sahihancin kowane labari da ya shafi Uwargidan Shugaban Ƙasa ta hanyar samun bayanai daga ofishinta ko hanyoyin da suka dace.