Cutar Ebola
Wani Ibo ne mai ciwon kanjamau ya je asibiti don ganin likita. Saboda bullar wata sabuwar cuta mai suna Ebola, Ibo bai yarda ya gaisa da kowa ba. Duk wanda ya miko masa hannu sai ya kada kai, alamar yana amsawa. Ana nan har layi ya zo daga wata Bayarbiya sai shi. Daga cikin ofishin likita da karfi aka kira sunan: “Bola.” Shi Ibo a tsammaninsa Ebola ake ce, kuma ana kiran mutum ne da sunan ciwon da yake da shi, sai ya yi wuf ya juya a guje, yana fadin “Chineke! I no touch Ebola o.” Yana nufin wai bai taba Ebola ba.
Daga Naseeru Taneemu Annuree (NTA), 08137284277
Ta gane ni
Wani dan giya ne ya je ya shawu, yana tafiya yana tangadi, yana ta suratai a hanya. Can sai ya ga wata akuya tana cin abinci, sai ya lallaba ya bude hannayensa ya rufe idanun akuyar. Sai akuya ta yi kuka “Bee!” Sai ya ce: “Ashe ta gane ni.”
Daga Azzubair M. Fagge, 080344412272
Yaro Jafar
Wata rana na sayo wa mahaifiyar Jafar cefane, sai ta ce mini: “Allah Ya biya ka.” Sai ya ce: “Mama, babanmu yana bin Allah bashi ne?”
Daga Sulaiman Mai Bazazzagiya, 08067917740
Halima
Wani mutum ne yake yi wa matarsa kuri wai shi jarumi ne. Rannan tafiya ta kama su, ya yi shirin yaki. Suna tafiya cikin wani daji sai ga dan fashi. Ya yi masu tsawa, suka tsaya cik. Da ya zo, sai ya tambayi matar sunanta, ta ce, Halima. dan fashin ya ce: “Kin yi sa’a, ban taba Halima, sunan mahaifiyata ne.” Ya juya wurin mijin, ya ce: “Kai yaya sunanka?” Sai ya ce: “Wallahi, ni ma ko gida Halima ake kira na kuma ka tambayi matata.”
Daga Amiru Isa Bakori, 08075959086