Jifar Buzu
Wani Buzu ne yazo wucewa ta wajen wasu mutane suna yin ginin gida na kasa. Buzu sai ya ga mutum daya a saman ginin, ga wasu mutum hudu a kasa suna ta jefa masa bulon kasa yana cafewa yana likawa a jikin Katanga. Ganin haka sai ya ce: “Arrr! Ku kauce, har ku hudu kun kasa jife mutum daya.” Ai kuwa Buzu sai ya dauki wata marmara ta bulo, ji kake daaaamm! Ya jefe na saman nan, ya fado kasa a some.
Buzu ya ware.
Muhammed Maikaset Kukawa, Jihar Borno
Lambar kati
Wani saurayi ne ya fi sati uku yana tura wa wata budurwa tes kamar haka: “Salam, masoyiyata, kawazucita, abin kaunata.” Ta ki amsa masa, sai ya aika mata da wadannan lambobin “88882034555522.” Kawai sai ta kirawo shi, ta ce masa: “Masoyina, katin MTN ne ko Glo?” Shi kuma sai ya amsa da cewa: “Ko daya, lambar katin zabena ce, ina son ki gwada da taki ko sun yi kama da juna?”
Daga Musa Manaja
Rashin sani
Wani saurayi ne da budurwarsa suna soyayya sai ta kai ziyara gidansu saurayin. Suna zaune suna hira sai ya ce bari ya sayo mta lemon kwalba. A lokacin nan Naira 50 ce kadai gare shi. Sai ya je wajen mai lemon, ya sayi Fanta kwalba daya, ya ari kwalbar 7up ya cika ta da ruwa. Yana zuwa ya mika mata Fanta ya rike 7up. Ita kuma sai ta ce: “Ai kuwa ni ba na shan Fanta, 7up nake so.”
Daga Muhammad Fagge
Bagobiri da Bature
Wani Bature ne ya zo Najeriya sai tafiya ta kama shi zuwa Sakkwato. A cikin tawagar da ta zo tarbarsa har da wani Bagobiri. Bayan sun gaisa sai Bature ya rike hannun Bagobiri yana kallon fuskarsa, yana mamakin irin tsagen da ke fuskarsa. Sai ya tambaye shi cewa: “Abokina, fada ka yi ne da damisa?”
Daga Danhadeja, Jihar Jigawa.
Kwaurin fatalwa
Wani mutum ne ya hadu da fatalwa, tsawonta har ba ya iya gano karshenta. Sai ya hau bishiyar dabino zai sare mata kai. Ya kai mata sara ke nan, a tunaninsa wuyanta ya sara, sai ya ji ta ce: “Wayyo kwaurina!”
Daga Jamilu Barde, Hotoro-Kano