✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

MU SHA DARIYA

Dan sane Malam Usman ne yana tsaye sai wani mutum ya sanya masa hannu cikin aljihu. Ya yi wuf ya cafke hannun, ya bata rai…

Dan sane

Malam Usman ne yana tsaye sai wani mutum ya sanya masa hannu cikin aljihu. Ya yi wuf ya cafke hannun, ya bata rai ya ce: “Don me ka sa hannunka a cikin aljihuna? Ya ce: “Ashana nake nema.” Ya ce masa: “Don me ba ka tambaye ni ba?” Ya ce: “Ba na magana da wadanda ban sani ba!”

Daga Maryam Abubakar 08036940511


Ba ni kadai ba ne

Wani jahili ne ya shiga sahun gaba a Sallar Asuba, da liman ya gama karatun Fatiha, sai kowa ya ce: “Amin!” Bayan dan lokaci sai alwallar Liman ta kare, sai ya miko hannu ya kama rigar na bayansa, wato wannan jahilin, yana nufin ya shiga gaba ya cikasa musu Sallah. Shi kuwa sai ya tsaya kerere, ya ce: “Haba liman, ai ba ni kadai na ce Amin din ba.” (Ya yi zaton laifi ya yi).

Daga mai lamba 08097154278


Mai talabijin

Wani mutum ne ya je wajen mai hada aure, domin ya samar masa matar aure, sai ya tambaye shi iriin matar da yake so. Shi kuwa ya bayar da siffarta kamar haka: “Ina son mace mai kyau, mai ilimi, wadda ta kware a iya wasanni da iya rawa kamar dan mazari da kida da waka. Kuma ina so idan ba na aikin komai, ta rika nishadantar da ni. Idan kuma zan huta, to sai ta yi shiru.” Mai hada aure kuwa ya ce masa: “Ai matar da kake son aure, ita ce talbijin ke nan.”

Daga Bashir Yahuza Malumfashi, 08065576011


Maganin DBD

Wani Buzu ne yana yawo yana tallar maganin gargajiya, sai wani ya kira shi ya ce masa: “Kana da maganin DBD?” Sai ya ce: “DBD mugun ciwo, shi ya kashe kakana shekara uku da ta wuce. Muna da maganinsa!”

Daga dahiru One-One Kubwa-Abuja 08033208651