✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu Sha Dariya

  Bagobiri a Kurmi Wani Bagobiri ne zai je Kurmi ci-rani, kafin ya tafi sai wani dattijo ya ce masa: “Idan ka je ka yi…

 

Bagobiri a Kurmi

Wani Bagobiri ne zai je Kurmi ci-rani, kafin ya tafi sai wani dattijo ya ce masa: “Idan ka je ka yi hankali da Jiga saboda in ka bari ta kama ka, za ka iya rasa kafarka ko kuma ka dade kana jinya.” Sai ya ce in sha Allah zai yi taka-tsan-tsan. Sai ya shiga daji ya samo sandar ga-ruwa saboda da ma sana’ar ga-ruwa zai yi a Kurmi. Bayan ya isa Kurmi da yamma ya kama hanyar masauki, yana cikin tafiya sai ga wani katon talo-talo ya yo kansa, yana tada gashi, yana kunburi. Shi kuma Bagobiri bai taba ganin talo-talo ba, sai ya tsorata. Ya zaro sandar ga-ruwa ya ce: “Hala kai aj Jiga ko? To bari in ji ma kafin ka illata min kafa. Ko can an ba ni labarinka.” Sai ya rafka masa sanda, Ya kashe shi.

Daga A’isha Abubakar S. Yakubu Abuja FCT

Za mu fasa

Wani dan acaba ne ya dauko wani dan sanda zai kai shi wurin aikinsa da sassafe, suna cikin tafiya sai dan achaba nan ya hango wata tirela ta gifta musu, gashi kuma ya debo a guje. Don haka sai ya ce da dan sandan nan: “Ofisa!” dan sanda ya amsa da cewa: “Ya aka yi ne?” Sai dan acabar nan ya ce: “Cire hularka ka rike a hannu.” dan sanda ya ce masa saboda me? Sai ya ce: “Ta karkashin waccan tirelar za mu bi . fasa!”

Tambaya da amsa

Wani jahili ne, bayan an gama Sallah, sai ya tambayi liman cewa: “Malam, ko za a iya yin alwalla da ruwan shayi?” Sai shi kuma liman ya amsa masa da cewa: “kwarai kuwa, za a iya, muddin dai za a iya yin Sallah a kan burodi!”

Daga Ahmad M. B. Umar, Kaduna 08131928213

dan kamasho

Wani dan hayis ne idan ya je tashar mota, kullum aka loda masa fasonja, ba ya ba ’yan kamasho hasafi, kamar yadda sauran direbobi ke yi. Wata rana ya cika motarsa da fasinja, har ma ya fara shirin tafiya, sai dan kamasho ya zo motar ya yi wa fasinjojin sallama, bayan sun amsa, sai ya ce musu: “Dama wani dan jawabi ne nake son yi maku, saboda duk abin da ya faru da ku a hanya, wajenmu za a dawo, don haka ina sanar da ku cewa direban motar nan yana da cutar farfadiya, don haka duk wanda ya ga zai amince ya hau, ruwansa, duk abin da ya faru kada a yi kuka da mu!” Rufe bakinsa ke da wuya sai fasinjoji suka yi ta fita daga motar, kafin ka ce wani abu, kowa ya kama gabansa,.

Daga Zaharaddeen Salisu 07062447413