✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu Sha Dariya

  Gasar tsere Wani matashi ne ya saba da gudu a babur, rannan ya tafi gun aiki, inda ya kai kilomita 25. Ya yi tafiyar…

 

Gasar tsere

Wani matashi ne ya saba da gudu a babur, rannan ya tafi gun aiki, inda ya kai kilomita 25. Ya yi tafiyar da ta kai kilomita 23, saura kilomita biyu kawai ya isa, kawai sai suka yi kiliya da wani matashi, shi ma yana tika gudu a nasa babur din. Yana ganin wannan matashi da yake gudu, kawai sai ya yi kwana ya bi shi. Da wancan ya waigo ya ga an biyo shi da gudu, sai ya kara wuta, domin kuwa bai son a wuce shi. Nan fa suka runtuma, suka yi ta gasar tsere a tsakaninsu. Sai da suka ci kilomita 20, sannan ya samu wuce shi, daga nan ya juyo domin tafiya wajen aikinsa. Ya ce: “Haba, ai da ban wuce shi ba, sai ya yi ta kurin shi mai gudu ne.

Sunusi Uban Kulob Garko Kano 07038766018

Manomin gyada

Wani manomi ne da yake tare da dansa, suna aikin gona. Da ya ga gyadarsa ta yi kyau sosai, sai ya ce wa babban dan nasa: “Bana zan sayi keke.” dan nasa sai ya ce: “Ni kuwa zan kada karaurawa ke nan.” Jin haka sai baban ya kai masa mari, ya ce masa: “Kana son ka bata keken ne?”

Daga mai lamba 08032859794

dan Mafara

Wani mutumin mafara ne ya je wurin malami, domin daukar karatu. Bayan an rubuta masa allo, aka biya masa, da zai tashi, sai malamin ya ce: Ka je ka yi ta yi.” Shi kuwa da ya amshi allonsa, sai ya koma gindin bishiya ya yi ta cewa: “Ka je ka yi ta yi, ka je ka yi ta yi.” Wannan wai shi ne karatun.

Daga Yazidu Mahmud Inuwa Iman 08062213814

Jirgi har daki

Wani Bafulatani ne ya je Saudiyya, aka sauke su a wani dogon otel, inda aka ba su daki a hawa na goma. Da zai hau sai suka hau lifta, haka ma da za su sauko. Bayan sun sauka kasa sai ya kalli saman benen ya ce: “Hodijam, wani abu sai Saudiyya, jirigi har a daki!” Ya dauka lifta da suka hau wai jirgi ne.

A.A. Azare Mazaunin Agege Legas 08066888222