✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

MU SHA DARIYA

  Soyayya ko yaudara? Wasu samari ne su biyu, Lukman da Surajo suna tafiya a kan hanya, suka zo wucewa ta gaban wani gida bene;…

 

Soyayya ko yaudara?

Wasu samari ne su biyu, Lukman da Surajo suna tafiya a kan hanya, suka zo wucewa ta gaban wani gida bene; sai wata kyakkyawar budurwa ta leko ta taga tana yi masu murmushi.

Lukman: “Kai Surajo, dubi wata kyakkyawar yarinya can tana mana murmushi.” Surajo: “kyale ta kawai, zo mu tafi.” Har sun yi gaba sai Lukman ya kara waigowa, sai ta yi masa alamun kira da hannu. Lukman: “Surajo, yarinyar nan tana kirana fa!” Surajo: “Ka kyale ta na ce, zo mu tafi.” Lukman: “Kai ko anya ba bakin ciki kake yi mani ba? Gaskiya sai na je.” Sai Lukman ya nufi gidansu yarinyar nan da ta yi masa yafuce da hannu, ta shigar da shi falo suka gaisa, ta kawo masa abinci da abin sha. Kafin ya fara cin komai sai suka ji mota ta tsaya a kofar gida. Budurwar ta leka taga, ta ce masa “Ga mijina nan ya dawo.” Lukman ya tashi a tsorace yana neman hanyar fita, sai ta ce masa: “Zo ka gani, dauki kayan nan ka fara guga, in ya shigo zan ce mai guga ne na kira.” Lukman ya kwashi tulin kaya ya ci gaba da guga, ya kwashe ranar gaba daya yana gugar kaya, amma sun ki karewa kuma mijin bai fita ba. Da safe sai Lukman ya hadu da abokinsa Surajo. Lukman: “Surajo ka san kuwa jiya wuni na yi ina guga a gidansu yarinyar nan kuwa?” Surajo: “Ba na ce maka kar ka je ba? Duk kayan nan da ka gani, ni na wanke su!”

Daga Bashir Yahuza Malumfashi, 08065576011

Gadin gawa

Wani malami ne mai gadin makabarta, sai aka kawo gawarwaki guda uku aka aje dakin ajiye gawa. Da aka zo daukar gawa daya daga cikin ukun, sai ya shiga ya bude masu kofa suka dauka.  Shi kuma sai ya koma ciki, domin ya gyara sauran, a wurin fitowa sai kofa ta rike masa riga. Maimakon ya juya ya ga abin da ya kama rigar, sai ya yi tsammanin ko gawa ce ta rike masa riga. Nan sai ya kama ihu da kururuwa kuma ya ki waigawa ya ga abin da ya kama masa rigar.

Daga Hussaini Sunshine Birnin Gwari, 08032824939

Hawan rakumi

Wani Bahadeje ne ya je wurin wani malami domin a yi masa fassarar mafarki, ya ce: “Malam na yi mafarkin na hau rakumi.” Sai malam ya ce masa: “Za ka shiga Aljanna.” Bahadeje ya ji dadi, sai ya ci gaba da cewa: “Ai malam in gaya maka, har ga tozonsa na je.” Jin haka sai malam ya ce: “Ka wucee Aljanna, ka shiga wuta.” Sai ya ce: “To, ai da na je sai na zamo kasa.”

Daga Musa Uke Karu, 08051702591