Hajiya Khadija Yahaya Shantali ’yar asalin Birnin Kebbi ce a Jihar Kebbi. Ma’ aikaciyar banki ce tun tana karamar ma’aikaciya har ta kai matsayin Manaja, a tattaunawarta da Aminiya ta ce tana son ganin mata suna taimaka wa mazansu a fannin da mace ta ga za ta iya taimaka wa mijinta:
Tarihin rayuwata
Sunana Khadija Yahaya Shantali ni ’yar asalin Jihar Kebbi ce kuma an haife ni a garin Birnin Kebbi a 1970, na yi makarantar firamare a Birnin Kebbi wadda ake kira yanzu Gwandu Emirate Firamare a 1977 daga nan na wuce Kwalejin ’Yan Mata (WTC) da ke Birnin Kebbi inda na yi wata uku kacal a makarantar daga nan mahaifina ya dauke ni zuwa Landan inda ya sa ni a wata makarantar sakandare mai suna Rosemead School, Little Hampton, Sussed England a 1983 -1988. Bayan na gama waccan makaranta na ci jarrabawata ta GCE sai na wuce makarantar Wood House Grobe Apery Bridge Brad Ford Understand Industries da ke Ingila daga 1988-1983, daga nan sai mahaifina ya dawo da ni gida Nigeriya inda na shiga Jami’ar Usman Dan Fodiyo da ke Sakkwato na yi Digiri kan Nazarin Halittu (Bsc, Biology) daga 1990-1995 a lokacin saboda yawan yajin aiki da ake yi shi ya sa muka dade ba mu gama makarantar ba. Bayan da na gama Jami’ar Usman Dan Fodiyo sai na wuce hidimar kasa (NYSC) inda aka tura ni Abuja na yi a wani banki da ake kira Inland Bank a Wuse Zone 4, Abuja.
Aiki
Bayan na kammala hidimar kasa sai bankin ya dauke ni aiki, ina aiki da bankin a Abuja sai aka turo ni zuwa gida Birnin Kebbi. A nan Birnin Kebbi na yi aiki da bankuna kamar haka First Inland Bank, Unity Bank, Enterprise Bank yanzu kuma ina aiki da Heritage Bank a matsayin Manaja ta Birnin Kebbi. Bayan da na dawo Birnin Kebbi ne sai na je Makarantar Kimiyya da Kere-Kere ta Waziri Umaru da ke Birnin Kebbi na yi Babbar Diploma a kan kasuwanci (PGD Business Administration) daga shekarar 2001-2002 saboda ba ni da kwarewar karatu a kan fannin kasuwanci kuma a shekarar 2007-2010 na sake komawa Jami’ar Usman Dan Fodiyo da ke Sakkwato na yi Digiri na biyu a fannin kasuwanci.
Kalubale:
Kalubalan da nake fuskanta a wurin aikina shi ne ni dai mace ce kuma ina da maigida da ’ya’ya, kafin in wuce wurin aiki sai na yi wa maigida abincin karyawa in kuma shirya yara zuwa makaranta, kuma kowa ya san aikin banki a bude da wuri kuma ba a rufewa da wuri. Kuma babban kalubalen da nake fuskanta shi ne tun ina ’yar shekara biyu an gano cewa ina da ciwon amosanin jini. Lafiya dai wata rana sai a hankali a hanakali yau ciwo gobe lafiya, amma duk da haka nan dai bai sanya ni kasa yin ayyukana ba, kuma ni kadai ce mace Manajan Banki a duk Jihar Kebbi. Wani kalubale shi ne idan kana Manajan Banki dole sai ka rika bin jama’a domin jawo abokan hulda wadansu ba su ganuwa da rana sai da dare a matsayina na mace mai aure wannan ba karamin kalubale ba ne, ko kana aiki bai kamata a ce an ga mace a wadansu wurare ba. Amma kana iya sanya abokan aiki su taimaka maka amma sai dai wadansu abokan aiki idan ka tura su wasu wurare in suka dawo ba za su fada maka gaskiyar al’amari ba, amma wadansu tantagariyar gaskiya za su fada maka.
Burina:
Burina shi ne in gaji mahaifina wajen aikin lauya domin mahaifina yana da kamfanin lauyoyinsa (Chamber), idan zai yi wasu aikace -aikace yana kirana, da ni ake yi na sani. Burina shi ne in na girma in zo in rike wannan Chamber tashi a matsayin lauya. Amma da Allah Ya sa na zo neman gurbin karatu a Jami’ar Usman Dan Fodiyo, Mai martaba Sarkin Bunza, Alhaji Mustapha Bunza da ya zo ya gan mu ’yan Arewa kuma na yi kimiyya da fasaha (Science and Art), kuma ana neman mata masu kimiyya ni kuma na cika ne ina son in yi karatun lauya sai ya kira mahaifina ya ce ya kamata a sa ni cikin mata masu yin kimiyya saboda ana neman mata masu kimiyya. Sai mahaifina ya yarda dalili ke nan ya sanya ban gaji mahaifina ba a aikin lauya. Daga baya kuma sai ga shi na koma Art saboda aikin banki.
Kungiyoyi:
Kungiyar da nake ciki kuma nake daukar nauyin kungiyar, ita ce, Kungiyar Masu Ciwon Amosanin Jini, mun kafa wannan kungiya saboda yara da iyayensu masu fama da ciwon amosanin jini, don taimaka wa kanmu. Domin ciwon akwai shi sosai a cikin wannan jiha ta Kebbi wannan kungiya tana taimaka wa masu ciwon amosanin jini muna rarraba magunguna kuma duk wata muna taro domin wayar da kan jama’a kuma muna taimakawa wajen yiw a wadansu aiki a cikin jikinsu. Ko a kwanan nan mun kashe Naira miliyan daya da dubu 200 wajen yi wa wadansu aiki a kafafuwansu.
Tarbiyya daga iyaye:
A gaskiya iyayena sai dai in ci gaba da yi musu addu’ar Allah Ya saka musu da alheri. Domin a kullum suna yi mini huduba cewa duk inda nake in zama mai hakuri, kuma duk yadda na ga mutum in mutunta shi in ya girme ni in ba shi girman da Allah Ya ba shi. Sukan ce mini kada in zama mai wulakanta jama’a a duk irin mukamin da na samu kuma in rika daraja mutum babba ko karami. A kan haka ne duk inda aka kai ni za ka ga ina mu’amala da jama’a kuma da zarar an canja ni daga inda nake aiki za ka ga jama’ar da muka yi aiki da su ransu yana baci. Ba komai ne ya jawo mini haka ba illa tarbiyyar iyaye da na dauka tun ina karama.
Shawara ga mata:
Shawara ga mata ita ce mata su fito su yi aiki ko kuma su samu wata sana’a, domin yanzu tattalin arzikinmu ya karanta, mazanmu nauyi ya yi musu yawa dole sai mu mata mun tallafa wa mazanmu da yaranmu. Kuma in kin samu dama ki taimaka wa sauran al’umma. Mata zama ba namu ba ne, akwai damar da Allah Ya ba mu da za mu taimaka wa mazanmu da iyayenmu da yaran da Allah Ya ba mu da sauran al’umma.
Mace bai dace ba a ce tana zaune ba ta sana’ar komai duk bukatarki sai dai ki dora wa maigida ga matsalolin yau da kullum sun yi yawa ga biyan kudin makaranta na yara ga kudin zuwa asibiti in ba a da lafiya ga kudin abinci da na tufafi da na sauran bukata ta yau da kullum. Abubuwan sun yi yawa dole ne mata su shigo su rika taimaka wa mazansu domin har yanzu a Arewa muna da matsaloli sosai a cikin gidajenmu dole sai mata masu hali sun shigo wajen taimaka wa gwamnati don rage yawan matasanmu da ke zaman banza musamman ’ya’ya mata. Kuma ina shawarta iyaye mata su rika tarbiyyantar da ’ya’yansu su rika sa su hanyar gaskiya domin ba yadda za a ce ki ce yaronki ya bar yin karya amma ke ba ki kauce wa yin karya ba, idan yaro ya tashi da kyakkyawar tarbiyya za ki ga ba ruwansa da shiga wani ta’addanci ko zalunci da makamantansu.
Haduwa da maigida:
Maigidana likita ne, a lokacin ina Jami’ar Usman Dan Fodiyo, Sakkwato na zo karshen karatuna ina rubuta kundin neman digiri sai malamina ya ce bari a ba ni yin bincike game da ciwon amosanin jini domin ni ina da wannan ciwo kuma ni kadai ke da shi a cikin ajinmu. Sai aka tura ni dakin yin gwajen-gwajen jini domin in gano masu dauke da irin ciwona. Ina zuwa ana ba ni jinin da aka tara ina aunawa domin gano masu irin wannan ciwo kamar cikin mutum dari mutum nawa ne muka samu da ciwon amosanin jini, sannan nawa ne suke da laulayi a cikin jikinsu da za su iya yada wa wadansu?
Ina cikin wannan aiki sai malamina ya ce ba mu samu ainihin yawan jama’ar da muke so ba, sai ya tura ni Asibitin Tunawa da Sarki Yahaya da ke Birnin Kebbi ta nan ne na hadu da maigidana Dokta Abubakar Balarabe Koko kuma a lokacin yana kawo yaransa muna aunawa domin yaransa na da amosanin jini, shi kuma likitan yarana ne, kuma yana zuwa wurinmu yana duba yara masu lauyayin jiki. To a nan ne muka hadu.
Abin da nake so a rika tunawa da ni:
A halin gaskiya abin da nake so a rika tunawa da ni, shi ne wannan kungiya da na kafa ta masu ciwon amosanin jini. Domin a lokacin da ina karama kafin a san cewa ina da wannan ciwo sai ka ga jikina wani wuri yana kumburewa ko a ce na yi targade ko karaya. A lokacin Baba yana da hali sai kawai ya wuce da ni kasashen waje inda aka gano ina da ciwon amosanin jini. To yanzu akwai masu irin wannan ciwo da dama a cikin al’umma kuma yawanci wadansu iyayensu ba su da kudin da za su saya musu magani, amma ta wannan kungiya tamu za su rika samun magunguna kyauta, wadansu har aiki muke sa wa ana yi musu. To kafa wannan kungiya ce nake son a rika tunawa da ni, ina fata ko ba mu da rai yaranmu su ci gaba da wannan aiki.
Tufafi:
Na fi sha’awar atamfa da leshi, sai dai mu aikinmu na banki ya ba mu tsarin irin kayan da za mu rika sanyawa idan za mu zo aiki in ban da ranar Juma’a.