✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu ribaci kwana goman farko na Zul Hijja -Falalu Dorayi

A yawaita sadaka da zumunci da taimakon marayu da azkar da nafilfili da karatun Alkur'ani.

Fitaccen darakta a masana’antar Kannywood, Falalu Dorayi ya yi kira da Musulmi su dage wajen ribatar kwana goman farko na watan Zul Hijja saboda matsayin kwanakin a wajen Allah.

Falalu ya bayyana hakan ne a shafinsa na Instagram, inda ya bayyana kwanakin a matsayin masu daraja da albarka.

Ya ce manzon Allah ya nuna cewa babu kwanaki da aikin alheri ya fi soyuwa a cikinsu irin wadannan ranaku.

“Kwana 10 Zul Hijjah kwanaki ne masu daraja da albarka, saboda matsayinsu a wajan Allah.

“A cikinsu Allah ta’ala Ya cika addini, kuma da cikar addini ne imani ya yi karfi sai munafurcin zuciya ya mutu.

“Da karfin imani mutum ke cin nasara a kan zuciyarsa wadda take ba shi umarni zuwa mummunan aiki.

“Mu yawaita ayyukan alheri irinsu sadaka da zumunci da taimakon marayu da karatun Alkur’ani da azkar da nafilfili.

“Kuma a kiyayi ayyukan sabo, domin mu dace da tarin alhwrai da albarkar da Allah Ta’ala Yake rabawa.


“Annabi (SAW) ya ce; “Mu karanta wani abu mai yawa na “Allah Akbar, Allah Akbar, Laa ilaha illal Laah, Allah Akbar, wa Lil Laahil hammd”, inji shi.


Daraktan ya kara da cewa azumin ranar Arfa sunna ce babba.

A karshe, daraktan ya ce, “Lallai wadannan kwanaki ne na rigeginiyar ayyukan alheri.

“Allah Ya yi mana afuwar kurakuranmu da munanan ayyakunmu. Allah Ya jikan iyayenmu da al’ummar Musulmi baki daya”, inji Falaki Dorayi.