✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Muna da cikakken aminci a kan INEC —Amurka

Amurka ba ta goyon bayan kowanne daga cikin dukkanin ’yan takarar Shugaban Kasa.

Gwamnatin Amurka ta sanar da cewa tana da cikakkiyar yarda da kuma aminci a kan Hukumar Zaben Najeriya (INEC) wajen sauke nauyin da rataya a wuyanta a yayin Babban Zabe na 2023 da ke tafe.

Mary Beth Leonard, Jakadar Amurka a Najeriya ce ta bayyana hakan yayin Taron Tattaunawar Daily Trust karo na 20 da ke gudana yanzu haka a Abuja.

Jakadar ta ce Amurka ba ta goyon bayan kowanne daga cikin dukkanin ’yan takarar Shugaban Kasa a zaben na watan Fabrairu, sai dai ta bukaci zaben ya kasance mai cike da adalci kuma a tabbatar ya gudana cikin lumana da aminci.

A cewarta, “Amurka tana goyon bayan duk wasu tanade-tanade na gudanar da zabe na gaskiya da adalci wanda zai yi daidai da ra’ayin al’umma kuma ya gudana cikin lumana.

“Muna da cikakkiyar yarda da aminci a kan Hukumar INEC wajen sauke wannan nauyi na gudanar da zaben.

“Zaben 2023 wata dama ce da Najeriya za ta ribata ta sake tabbatar da a kanta a matsayin jagorar dimokuradiyya a nahiyyar Afirka.

“Ba ma goyon bayan kowanne daga cikin ’yan takara amma muna goyon bayan duk wani tsari da zai tabbatar da an gudanar da sahihin zabe na gaskiya cikin lumana.

“Wannan shi ne tubalin dimokuradiyya kuma hanya sahihiya ta sauya shugabanci.

“Yana da muhimmanci mu waiwaya kan yadda tun daga shekarar 1999 zuwa yanzu, ’yan Najeriya suka rika samu nasarar kwankwadar romon dimokuradiyya wanda ya yi daidai da ’yancinsu na kasancewa ’yan kasa.

“Fiye da tsawon shekaru 20, Najeriya ta nuna wa Afirka da ma Duniya baki kwazonta na gudanar da zabe cikin lumana da gaskiya.”

Mary Beth ta ce a yayin da ake yi wa tsarin dimokuradiyya zagon-kasa wasu wuraren da dama a Afirka, Najeriya ta yi tsaya tsayin daka wajen tabbatar da wanzuwarsa.

A nasa jawabin na yi wa manyan baki maraba, Malam Kabir Yusuf, Shugaban Majalisar Gudanarwa na Kamfanin Media Trust Limited masu wallafa jaridar Daily Trust da Aminiya da sauransu, ya ce taron tattaunawar na bana na musamman ne wanda ya zo a kan gaba yayin da Babban Zabe ya rage wata guda kacal.

A cewar Malam Kabir, Taron Tattaunawar wanda Kamfanin Media Trust Limited ya saba daukar nauyi duk shekara, wata ’yar gudunmuwa ce da kamfanin yake bayarwa wajen assasa zaman lafiya a kasar.

Aminiya ta ruwaito cewa, Taron Tattaunawar na bana mai taken: Bibiyar Manufofin ’Yan Takarar Shugaban Kasa a 2023, na gudana ne kai tsaye a Cibiyar Taro ta Sojin Sama da ke Abuja, wato NAF Conference Center.