✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mu leka rayuwar matan aure masu yoyon fitsari

Cutar yoyon fitsari tana samuwa ne a dalilin doguwar nakuda.

Bincike ya nuna cewa dubban mata ne a fadin kasar nan suke fama da cutar yoyon fitsari.

Cutar yayon fitsari cuta ce da ke haifar da fitar fitsari ba tare da tsayawa ba, lamarin da ke sa masu cutar shiga halin damuwa.

Binciken da aka gudanar a fannin kiwon lafiya ya nuna cewa a mafi yawan lokuta cutar yoyon fitsari tana samuwa ne a dalilin doguwar nakuda da yin tiyata ga mata da kuma wasu abubuwa da suka shafi al’ada.

Mata da yawa sun rasa ransu sanadiyyar cutar, kuma yayin da wasu suka warke daga cutar, wasu da dama suna zaune ne a cikin rashin tabbas sakamakon an yi musu aiki amma ba su warke ba.

Binciken Aminiya ya gano cewa bayan ita kanta wannan lalura da matan da suka kamu suke fama da ita, a gefe guda wasu daga cikinsu suna kamuwa da matsalar daukewar jinin al’ada wanda hakan ke sanya fargaba a zukatansu, lura da cewa idan mace ba ta jinin al’ada babu batun daukar ciki gare ta.

‘Yadda ake nuna mana kyama saboda cutar yoyon fitsari’

Fatima Kamal da ke garin Burum-Burum a Jihar Kano, kuma take da kimanin shekara 18 da haihuwa, ta ce ta kamu da cutar yoyon fitsari ne bayan shafe kwana hudu tana nakuda.

“A asibiti ne aka shaida mini cewa ba zan iya haihuwa ba sai dai a cire min dan.

“Sai rashin gado ya sa muka nemi wani asibiti mai zaman kansa, su kuma suka ce mu je Asibitin Koyarwa na Aminu Kano inda a can aka karbe mu aka yi min aiki aka cire jaririn, amma ya riga ya mutu.

“Bayan an sallame mu, mun koma gida sai na fuskanci shimfidata tana jikewa sai muka je asibiti inda suka fada mana cewa na kamu da wannan cuta.

“Tun daga wancan lokaci na shiga damuwa na rashin tabbas din yadda rayuwa za ta kasance min a nan gaba.

“Yanzu an yi min aiki amma ban warke ba don haka ina sa rai a sake yi min wani aikin nan gaba saboda ina cikin damuwa.

“To ko mutum da yake tare da lalurar yana kyankyamin kansa ballantana wanda yake kusa da shi,” ta fadi cikin hawaye.

Ita ma Abasiyya Ado da ta kamu da wannan cuta kuma take jinyar aikin da aka yi mata, ta ce ta kamu da cutar ce a yayin haihuwarta ta fari.

“Na fara nakuda tun safe har zuwa dare ban haihu ba. Sai aka kai ni Asibitin Tsanyawa.

“A nan ma haihuwar ba ta zo ba. Daga nan suka mayar da mu Asibitin Bichi. Da suka ga ban haihu ba, sai suka yi min aiki aka cire dan sai dai babu rai.

“Bayan an sallame mu daga asibiti mun koma gida sai na fara ganin fitsari yana zuba a jikina ba tare da sanina ba.

“Da farko mun yi zaton saboda an sa min robar fitsari a lokacin da aka yi min aiki shi ya sa fitsarin yake zubo min sakamakon ya saba biyo robar.

“Da aka yi kwana biyu muka ga abin ya ci gaba sai muka koma asibitin.

Da suka ga matsalar sai suka tura mu Asibitin Zana, daga nan su kuma suka turo mu nan inda aka yi min aikin gyara,” in ji ta.

A cewar Abasiyya mijinta yana kulawa da ita domin shi ya kai ta aibiti da kansa.

“Gaskiya alhamdulillah. Mijina yana kulawa da ni sosai. Shi ya kawo ni asibitin nan kuma yana tsaye a kaina. Ina fata Allah Ya sa in warke,” in ji ta.

Ita ma Fa’iza Aliyu ta bayyana wa Aminiya cewa ta samu wannan laura ce a lokacin haihuwarta ta hudu.

Ta ce, “Na dauki lokaci ina nakuda a gida. Kasancewar duk ’ya’ya ukun da na haifa a gida na haife su, to a wannan lokacin ma ban je asibiti ba.

“Da na ga nakudar ta yi tsawo, sai na sha wasu magungunan gargajiya amma duk da haka haihuwa ba ta zo ba. Daga baya na haifi ’yata.

“Sai dai daga baya na lura idan na zauna ina jikewa hakan ya sa muka je Asibitin Tofa, su kuma suka turo mu nan. A yanzu ga shi an yi min aiki.”

A cewar Fa’iza tana samun kulawa daga mijinta domin shi ne ma ya kawo ta asibiti kuma yake daukar nauyin dukkan dawainiyar maganinta.

Halima Sa’adu wata mata da ta shafe shekara 15 da cutar yoyon fitsari ta shaida wa Aminiya cewa duk da cewa an yi mata aiki sau biyu har yanzu ba ta warke daga cutar ba.

A cewarta bayan ta dawo gida ta fuskanci kyama da surutai daga al’umma lamarin da ya sa ta shiga damuwa “Bayan da muka dawo gida na yi fama da masu zuwa tsegumi wanda hakan ya sa na daina fitowa tsakar gida don kada a gan ni a tafi ana gaya wa mutane.

Sai ya zama ko lokacin da zan yi wankin tsommokaran da nake amfani da su wajen tare fitsarin sai dai in shanya su a cikin daki don kada a gani.

Amma a yanzu da yake an adauki tsawon lokaci na riga na saba ba na damuwa da kymar da ake nuna min don wasu ma a yanzu zato suke yi na warke gaba daya, saboda ina iya shiga mutane,” in ji ta.

Wata matashiya mai suna Yasira Musa daga Minjibir ta ce ta kamu da wannan cuta ce sakamakon rashin asibiti a garinsu lamarin da ya tilasta ta shafe kwanaki tana nakuda.

“Lokacin da na fara nakuda ba a yi batun tafiya asibiti ba domin babu asibiti a kusa da mu.

“Sai dai da aka ga abin ya dauki tsawon lokaci ban haihu ba, shi ne aka dauke ni aka kai ni Asibitin Minjibir.

“A asibitin ne aka fitar min da jaririn inda a karshe dan ya rasu. A asibitin ne na fara ganin wani ruwa yana bin jikina tun daga wannan lokaci na san ina da yoyon fitsari.

“Na yi kuka matuka lura da halin da masu wannan cuta suke shiga na wulkancin maza da sauransu,” in ji ta.

Ta ce “Bayan wahalar da na sha na rasa dan, ga shi kuma har yanzu lafiyar ba ta samu ba, bayan kashe kudi masu yawa da muka yi.

Yanzu ina fata idan an yi min aiki ya kasance na warke sarai.”

Wata mai suna Fatima Abdullahi Yaryasa ta ce ta kamu da wannan cuta ce dalilin doguwar nakuda da ta fuskanta.

A cewarta, bayan aikin da aka yi mata ta warke kuma ta yi aure tana tare da mijinta har ma ta sake haihuwa.

“Daga baya na sake yin aure inda na haifi dana amma hakan ta faru ne karkashin kulawar likitoci.

“Domin tunda na samu ciki likitoci suka nemi in mayar da hankali wajen kula da lafiyata har zuwa lokacin haihuwa.

Tun kafin nakuda ta yi nisa na tafi asibiti aka cire min dan lami lafiya,” in ji ta.

Ita ma Tsaharatu Mansur Madobi ta ce duk da cewa haihuwar farko ce amma ta haihu ita kadai ce ba tare da taimako daga kowa ba.

“Ni kadai ce a gida lokacin da nakuda ta same ni, ina nan ina nakuda har na haihu. Dan ya yi ’yan awanni kafin ya rasu.

“Bayan na haihu da kwana uku kuma sai na fahimci cewa na kamu da cutar yoyon fitsari.

“Daga nan aka kai ni asibiti inda aka yi min aiki,” in ji ta.

Ta ce, “An yi min aiki sai dai ba a samu nasara ba. A yanzu haka ina sa ran za a sake yin wani aikin ko Allah zai sa a dace.”

Dukkan matan da Aminiya tattauna da su sun nuna cewa cutar ta jefa rayuwarsu cikin kunci da damuwa.

Dalilin da wasu matan ba sa a warkewa ko an yi tiyata —Likitoci

Dokta Amiru Imam Yola babban likita ne da ke kula da bangaren masu cutar yoyon fitsari a Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano, ya ce, “Cutar yoyon fitsari cuta ce da ke samun mata a dalilin budewar mafitsara lamarin da ke sa fitsari ya rika zuba ba tare da saninta ba.

Haka kuma cuta ce da za a iya yin riga-kafinta ta hanyar kula da mai juna biyu tun daga lokacin daukar ciki har zuwa haihuwarta.”

A cewar Dokta Amiru matan da ke fama da cutar yoyon fitsari sun kasu kashikashi gwargwadon girman hudar da suka samu a jikinsu.

“Ana samun matan da hudar da suka samu ba ta da yawa, wannan za ki ga da zarar an yi musu aiki suke warkewa.

“Yayin da wasu kuma sai sun dauki lokaci wasu kuma saboda girman da hudar ta yi, to sai an yi aiki a matakai daban-daban.

“Akwai kuma wadanda saboda yadda ciwon ya same su sai an yi musu dashen gaban nasu ma gaba daya sannan a zo a yi aikin yoyon fitsarin.

“Akwai kuma wadanda sai dai su yi hakuri da halin da suka samu kansu a ciki, domin an yi aikin sai dai irin wadannan kadan ne a cikin dubbai,” in ji shi.

Dokta Amiru ya kara da cewa idan har masu cutar suka bi dokoki sukan samu saukin lalurar.

“Idan matan suka rika shan ruwa sosai, to hakan yana dauke musu zarnin fitsarin.

“Haka kuma idan ba su daukar abu mai nauyi to za su samu waraka cikin yardar Allah.

“Sai kuma muhimmin abu shi ne kula da kansu wajen tsabta,” in ji shi.

Dokta Amiru ya ce idan mace ta warke daga yoyon fitsari za ta iya ci gaba da haihuwarta ba tare da matsala ba.

Cutar tana karuwa kullum —Kungiyoyi

Malam Musa Isa, shi ne Shugaban Gidauniyar Kula da Masu Yoyon Fitsari ta Fistula Foundation Nigeria da take aiki da hadin gwiwar Asusun Kula da Yawan Jama’a na Majalisar Dinkin Duniya (UNFPA) Gidauniyar Fistula da ke Kalifoniya a Amurka wajen kokarin tallafa wa rayuwar masu wannan cuta da yi musu aiki kyauta da sama musu abin dogaro da kansu.

Ya ce, “Kungiyarmu ta Fistula Foundation mun kai shekara 25 zuwa 30, muna yin ayyukan da suka shafi ilimintar da al’umma game da wannan cuta ta yoyon fitsari, inda muke shiga lungu da sakon kasar nan don wayar da kan mutane kan yadda za a kauce wa wannan cuta.

“A yawancin lokuta idan mun je domin ilimintarwar sai mu samu mata masu yawa suna tare da cutar, amma ba su nemi magani ba ko kuma ba su dace da aikin ba.”

“Kuma bayan mun yi musu aiki muna tsugunar da su mu koya musu sana’o’i ta yadda za su tsaya da kafafunsu idan sun koma cikin al’ummarsu.

“Mun fahimci cewa matan da suka kamu da cutar sukan rasa kudadensu wajen neman magani, don haka akwai bukatar a taimaka musu su farfado, darajarsu ta dawo a tsakanin al’umma,” in ji shi.

Baya ga wannan kungiyar tana horar da likitoci da ma’aikatan jinya kan sanin makamar aiki wajen tallafa wa matan da suka kamu da cutar.

A cewarsa a bara sun yi wa mata 1,573 da ke dauke da wannan cuta aiki, kuma a yanzu haka suna kan yi wa mata masu yawa a bana a jihohi daban-daban na kasar nan.

Malam Musa ya kara da cewa kungiyarsu tana kai ziyara ga al’ummomin da masu cutar suka fito domin wayar musu da kai kan illar kyamar da suke nuna wa masu cutar.

Da yake bayani game da yadda matan ke kamuwa da cutar, Malam Musa ya ce duk da bincike ya nuna cewa matan sukan kamu kamu da cutar ce a dalilin doguwar nakuda amma a gefe guda wasu matan sukan kamu da cutar ce a dalilin aikin cire musu jarirai da ake yi asibitoci.

Ya ce cutar ba ta da alaka da auren wuri, “Domin akan samu matar da ta yi shekara 25 da haihuwa ko a ga wacce ta yi haihuwa biyar amma ta kamu da cutar.

Haka kuma wannan cuta ba ta kebanta da wata kabila ba, kamar yadda wasu ke dauka cewa wai cuta ce ta ’yan Arewa.

“Zan iya tunawa lokacin da muka je jihohin Kuros Riba da Oyo, sun so su hana mu yin aiki, wai a cewarsu ba su da masu wannan cuta.

“Amma zuwa lokacin da muka yi sanarwa a rediyo cewa za mu yi aiki, sai ga mata suna ta tuttudowa,” in ji shi.

Malam Musa ya ce idan gwamnati da hukumomi ba za su yi abin da ya kamata a bangaren lafiya ba, to batun dakile yawaitar cutar yoyon fitsari ba mai yiwuwa ba ne.

“Akwai bukatar gwamnati da hukumomi su yi abin da ya dace wajen kyautata harkar haihuwa ga mata.

“Akwai bukatar mai juna biyu ta samu kulawar da take bukata tun daga lokacin da ta dauki ciki har zuwa haihuwarta.

“A samu asibiti a kusa a wadata asibitin da duk kayan aikin da ake bukata.

“Haka idan bukatar zuwa wani asibiti ta taso ya zama akwai mota da ke jira ta dauki marasa lafiya.

“Shi ma asibitin da za a je a tabbatar komai akwai a kasa tun daga kan likitoci har zuwa kayan aiki da sauransu.

“Idan ba a samar da kyakkyawan yanayin haihuwa ga mai juna biyu ba, to za a ci gaba da samun karuwar wannan cuta a tsakanin matanmu, tunda dai ba a daina haihuwa ba,” in ji shi.

Gwamnati na kokarinta a Kano —Kwamishina

Kwamishinar Harkokin Mata da Walwalar Jama’a ta Jihar Kano, Dokta Zahra’u Muhammad Umar ta ce gwamnatin jihar tana iya kokarinta wajen inganta rayuwar matan da suka kamu da wannan cuta, inda ta ce gwamnatin na bayar da taimako ga matan don su samu su tsaya da kafafunsu.

“Bayan an yi musu aiki muna ajiye su a Cibiyar Lalura da ke Kwalli.

“A nan suke zama su yi jinya har su warke, idan sun warke gwamnati da hadin gwiwar kungiyoyi masu zaman kansu da suke bayar da taimako muna koya musu sana’o’i tare da ba su tallafin jari domin idan sun koma cikin al’ummarsu su iya tsayawa da kafafunsu,” in ji ta.

Masu cutar za su samu ladan hakuri —Sheikh Ibrahim Khalil

Da yake amsa tambayar Aminiya kan yanayin cutar da ibada, Sheikh Ibrahim Khalil ya shawarci matan da suka kamu da cutar su dauki lamarin a matsayin kaddara tare da mayar da lamuransu ga Allah.

“Idan suka yi hakuri suka mayar da lamuransu ga Allah, za su samu lada.

“Kuma akwai bukatar mutane su karbe su tare da ba su duk irin taimakon da suke bukata.

“Mu sani cewa wannan cuta ce daga Allah kuma za ta iya samun kowa.

“Ina kira gare mu da mu karbe su tare da tausaya wa halin da suke ciki,” in ji Shehin Malamin.