Gidan marigayi Alhaji Ahmed Mai Deribe da aka fi sani da Fadar Deribe ko Deribe Palace, ko Gidan Deribe gida ne da ya shiga kundin tarihi a duniya sakamakon yadda aka cudanya ruwan zinare wajen gina wasu sassansa. Tafkeken gida ne da ke kunshe da sassa daban-daban, inda yake da manyan sassa biyar da suka kunshin sassan mai gidan da na matansa hudu.
Shi ne gida mafi tsada kuma mafi kyau a Afirka a lokacin da aka gina shi, sannan yana cikin manyan wurare 20 na duniya masu burgewa. Gidan ya jawo hankalin manyan mutane daga duniya zuwa Maiduguri.
Fadar Deribe ta karbi bakuncin Mai martaba Sarki Juan Carlos I na Spain, wanda ya kwana biyu a gidan a 1986, wanda kuma bayan ziyartar gidan ya bayyana cewa, al’ummar Borno suna da tarihin fasahar zanen gidaje da kasarsa Spain tun shekara dubu da suka gabata.
Har wa yau Gidan ya karbi bakuncin Yarima Charles na Ingila da matarsa marigayiya Gimbiya Diana da tsohon Shugaban Amurka George W. Bush da tsohon Firayi Ministan Kanada da sauran wadansu fitattun mutanen duniya.
Gidan tamkar shi ne Taj Mahal din mutanen Borno da Najeriya da Afirka.
An fara aikin gina wannan gida ne a farkon 1980, inda a kan wani babban fili da daya daga cikin ’ya’yan marigayin da Aminiya ta tattauna da shi Alhaji Shettima Abubakar Mai Deribe ya ce ba zai iya tantance girman filin ba.
A cewar Abubakar Ahmed Deribe gidan mai beni biyu na da dakuna masu yawa, amma a bangarorin mata da mahaifiyar marigayin kowanne sashi yana da dakuna 4 da bayan gida a kowanne daki, sannan da dakin masu aiki, haka akwai wurin dafa abinci, wanda shi ma sashinsa daban. “A gaskiya ba zan iya cewa ga adadin dakunan da ke gidan ba, domin ka ga wani sashin idan ka shiga tamkar dakin taro yake amma kuma ba dakin taro ba ne, ka shiga ka ga yadda tsarin yake, in dai dakin kwana ake magana, idan ka debe na iyayenmu mata da kuma na samari da na masu aiki da na saukar baki, dakunan na da yawa ba ni da kiyasin adadinsu, domin gidan nan tamkar wata ma’aikata yake,”inji Abubakar Deribe.
Ya ci gaba da cewa: “Kusan kowanne bangare akwai filin ajiye mota, amma babu wani takamaiman wuri, in ban da inda shi mahaifinmu yake ajiye nasa motocin, kowa na ajiye motarsa a duk inda ya ga dama, domin yawan filin da ke gidan, idan ka tashi da safe za ka dauka wurin sayar da motoci ne.”
Aminiya ta gano cewa kujeru da gadaje da teburan zaman gidan wani fitaccen kamfanin sana’anta su a duniya mai suna Giobanni Monzio Compagnoni (GMC) da ke kasar Italiya ne ya yi su. Wannan kamfanin samar da kayyayyakin kawata daki fitacce ne wajen kawata gidajen mutanen da suka cika-suka batse a duniya kamar marigayi Sarki Fahad bin Abdul’aziz na Saudiyya da marigayi Shugaba Omar Bongo na Gabon da Sultan Kaboos bin Sa’id na Oman day a rasu kwanakin baya da Sheikh Khalifa Al Nahyan Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da kuma Babban Bankin Kuwait.
Kamar yadda Abubakar Mai Deribe ya shaida wa Aminiya an gina wannan gida na Deribe Palace ne a daidai wurin da aka haifi marigayi Alhaji Ahmed Mai Deribe, ya ce nan kauyen da iyayensa suka haife shi, kafin daga baya ya tashi ya koma Unguwar Fezzab a birnin Maiduguri.
Gina wannan gida ya kara fito da sunan Mai Deribe da ita kanta Jihar Borno da Najeriya a idon duniya ganin yadda aka narka makudan kudi wajen gina gidan wanda aka shafe shekara 10 ana yi babu fashi idan ka debe ranakun Lahadi kamar yadda Abubakar Deribe ya shaida wa Aminiya.
Game da halin da gidan Deribe Palace ke ciki da yadda aka gina shi, Alhaji Shettima Abubakar Ahmed Mai Deribe, ya bayyana wa Aminiya cewa: “Ainihin gidan nan ne inda aka haifi mahaifinmu, gidan yana da girma sosai akwai bangarori da dama da sassan da mahaifinmu yake da mata hudu da kuma gidan mahaifiyarsa. Ya zauna a wannan gida kusan shekara 12 kafin Allah Ya yi masa rasuwa, ya kuma yi rayuwarsa da iyalansa a gidan, wanda a wannan gida ne tsohon Shugaban Kasa (Cif Olusegun) Obasanjo ya kwana. Saboda lokacin da za a bude gidan, bayan kammala gininsa tsohon Shugaban Kasa na lokacin (Janar) Ibrahim Badamasi Babangida ya jagoranci wadansu shugabannin kasashen waje zuwa bikin bude gidan.”
Alhaji Abubakar Mai Deribe ya ce gaskiya ne cewa duk wani abu na kayan kawa an sa a gidan, kuma an kashe kudin da ya kai Naira biliyan daya wajen gina gidan a wancan zamanin.
“Maganar zinare da sauran kayayyaki masu daraja duk an yi amfani da su a cikin gidan kama daga tayil da aka hada shi da ruwan gwal da kafet da wajen rataye labule da kan famfo, kai hatta jikin kofar shiga babban falo, akwai gwal. Sannan ita kanta babbar kofar shiga cikin Palace bindiga ba ta ratsa ta wato (bullet proof) ce,” inji shi.
Yadda Mai Deribe ya rayu a gidan
Alhaji Abubakar ya ce, mahaifinsu mutum ne da ba ya shiga harkar mutane, babu ruwansa da rigima da kowa, harkar kasuwancinsa ce abin da ya sa a gaba, “Amma idan aka taba shi, gaskiya ba ya da dadin karo.
Amma yana da saukin kai wajen yin mu’amala da jama’a, kuma ba ya son cin amana da karya,” inji shi.
Ya ce: “Rayuwar mahaifinmu da iyalansa a cikin gidan, tana da ban sha’awa, mun yi rayuwa mai dadi da farin ciki tare da mahaifinmu, wanda shi mutum ne da ba ya son wargi, kuma yana sa ido sosai a kan rayuwar ’ya’yansa. Duk lokacin da aka yi Sallar Magariba, bai ga daya daga cikin ’ya’yansa ba, zai tambaya ina wane? Kuma a kullum yana fita ofishinsa, inda kowane yaro, zai je ya gaishe shi da misalin karfe 10 na safe. Haka idan dare ya yi dole ku hadu, mu samarin da ba mu da aure mu ci abinci tare, kuma idan ba a ganka ba, ka san abin da zai biyo baya.”
“Ni kaina haka ya taba faruwa da ni a 1996, ya ba ni sabuwar mota, to rana daya na bata lokaci a waje, na shiga gida an idar da Sallar Magariba. Da aka zo Sallar Isha, ya tambaye ni, ina na je bai gan ni a lokacin Sallar Magariba ba, sai na ce masa ina hanyar zuwa gida ne Magaribar ta same ni. Sai ya tambaye ni, ba ni da agogo ne? Nan dai na yi shiru, bayan kwana biyu sai ya kira ni, ya yi min fada sosai, sannan ya ce ina makullin motata? Na nuna masa, sai ya ce in ajiye a kan tebur, in tashi in fita. To haka duk wanda ya yi laifi, komai girmansa zai hukunta shi. A gaskiya rayuwarsa tana da ban sha’awa da ban mamaki, domin duk yawanmu, mu 27 yana kula da yadda kowa yake tafiyar da harkokinsa,” inji Abubakar Mai Deribe.
“Mu ’ya’yansa 27 ya rasu ya bari, amma jikoki gaskiya idan na ce maka akwai jikoki kaza na yi karya. Muna da yawan gaske mu ’ya’yansa da jikokinsa,” inji shi.
Game da rade-radin cewa ’yan gudun hijira sun mamaye gidan, Abubakar Mai Deribe ya ce, ’yan gudun hijira ai ko’ina akwai su a cikin Maiduguri, “Akwai ’yan gudun hijira a nan, amma duk wanda ka gani a cikin gidan nan, an ba shi wuri ya zauna dan uwanmu ne, Wadadansu suna zaune a wasu garuruwa ko kauyuka a dalilin rikicin Boko Haram suka bar inda suke, ka ga dole su taho inda muke, mu ba su wurin zama. Akwai ’yan uwanmu da Boko Haram suka kora daga garuruwansu da muke zaune tare da su a nan gidan,” inji shi.
Halin da gidan yake ciki a yanzu
“Ka san gidan ba zai taba zama daya da lokacin da marigayi ya gina shi yake ciki ba. Ko kula da gidan wani aiki ne mai zaman kansa. Gaskiya wasu wurare a gidan suna nan kamar yadda suke tun lokacin da aka gina shi, amma yau da gobe ba ta bar komai ba, ka ga yadda yanayin da gidan yake ciki da idonka, kuma kowa na kula da sashin da aka ba shi, to ka ga idan ka bar naka ya lalace laifin kai wanda ke cikinsa ne. Sai dai kamar yadda na fada maka, gidan na cikin yanayin ba yabo ba fallasa,” inji Abubakar Deribe.
Bai yi wasiyya kan gidan ba
Game da ko marigayin ya yi wasiyya kan gidan, Abubakar ya ce: “Mu ’ya’yansa a sanina da shakuwar da na yi da shi, ban ji ya yi wata wasiya a kan wannan gida ba, ka ga dai yadda gidan yake, zan iya cewa tun kafin Allah Ya karbi ransa ya raba mana gidan, kowa aka ba shi nasa sashin. Wannan ainihin Palace babu wanda aka ba, an bar shi ne a matsayin na iyalai duka. Mu ’ya’yansu 27 kullum kanmu a hade yake, tun rasuwarsa har yau da nake magana da kai, ba a taba samun wani ya je kotu, ko wani wuri a kan maganar gado ba. Tunda ya ba kowa sashi a cikin gidan maganar raba gida ba ta taso ba. Shi babban yayanmu wato Alhaji Zanna tun ana gina gidan aka gina masa bangarensa amma ba yana cikin Palace ba ne.”
Shi kuwa Ba’ana wanda shi ke kula da sashin Palace din, kuma wanda ya zaga da Aminiya sassan gidan, ya ce yana zaune a gidan ne tun ana gininsa, kuma ya zauna da marigayi Alhaji Mai Deribe shekaru da dama. Ba’ana ya bayyana marigayi Mai Deribe da mutum mai kaunar jama’a da taimakonsu. Ya ce a yanzu haka shi ke kula da wannan sashi na marigayi Alhaji Ahmed Mai Deribe, kama daga manyan falo sama da 10 da kuma dakunan kwanansa da wurin karbar baki,wadanda duk a yanzu suka zama tamkar wani wuri na tarihi da baki ke kawo ziyara.
An haifi Alhaji Ahmed Mai Deribe ne a 1924, kuma ya rasu a ranar 13 ga Maris din shekara ta 2002 yana da shekara 78 a duniya a birnin Makka na kasar Saudiyya inda ya je jinya, kuma an yi masa Sallar janaza a Masallacin Ka’aba. Allah Ya jikansa da rahama.