✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu koma tafarkin Manzon Allah don mu rabauta —Sanusi II

Ya kamata al’ummar Musulmi su hada kai wajen neman ilimi domin inganta rayuwarsu.

Shugaban Darikar Tijjaniya ta Jam’iyyatu Ansariddeen, Khalifa Muhammadu Sanusi, ya shawarci al’ummar Musulmi a kan ka da su bari lokaci ya kure ba tare da sun koma kan tafarkin Manzon Tsira, Annabi Muhammadu (SAW) ba.

A cewar Sarkin Kano na 14, riko da koyarwa da kyawawan dabi’u gami da tabbatuwa a kan tafarkin Annabi Muhammad (SAW), ita ce kadai hanyar da za ta magance duk wasu matsaloli da ake fuskanta a rayuwarmu da kuma zamantakewa.

Wannan furuci na Khalifa Sanusi na zuwa ne a cikin jawaban da ya gabatar ranar Juma’a a Lakwaja, babban birnin Jihar Kogi, a taron bikin Maulidi na shekara-shekara karo na hudu da aka gudanar domin karamci ga fiyayyen halitta.

Bayanai sun ce an gudanar da taron bikin Maulidin ne a kan wani maudu’in da ke nuna cewa mafitar duk wani abu da ya shige wa dan Adam cikin duhu ita ce komawa kan tafarkin Cikamakin Annabawa da Allah Ya turo wa Zamanin Karshe.

Khalifa Muhammadu Sanusu, Gwamna Yahaya Bello da sauran manyan malamai da shugabanni a wurin bikin Maulidin

Khalifa Sanusi wanda ya yi karin haske kan jawaban da Sheikh Mulid Mahy ya yi a taron, ya ce ya kamata al’ummar Musulmi su hada kai wajen neman ilimi domin inganta rayuwarsu da kuma al’umma baki daya, yana mai cewa ilimi shi ne hasken fitilar da ke yi wa kowane mutum jagoranci.

Ya kuma yi kira ga mabiya Darikar Tijjaniya kan cewa su yi riko na gaskiya da koyarwar Annabi Muhammadu (SAW) domin a cewarsa hakan ne kadai zai sa rayuwarsu ta tabbata a matsayin salihan bayi cikin Musulmi.

Kazalika, tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya ya yi kira ga dukkan Musulmi da su dage da addu’a su kuma kasance masu riko da gaskiya sannan su zama masu tawali’u da nesantar munanan ayyuka.