✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu hada hannu wajen gina Sakkwato —Zababben Gwamna

Ya bukaci PDP da sauran jam'iyyu su hada hannu don yin aiki tare.

Zababben Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu ya nemi goyon bayan jam’iyyar PDP da sauran jam’iyyun siyasa da su hada hannu wajen sake gina jihar.

Aliyu ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, bayan shi da Mataimakinsa Idris Mohammed Gobir, sun karbi shaidar lashe zaben gwamna da mataimaki na jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.

Sauran zababbun ‘yan majalisar jihar 30 da suka lashe zabe sun karbi shaidar lashe zaben a ofishin INEC da ke kan titin Tangaza a jihar.

Jam’iyyar APC na da ‘yan majalisa 20, yayin da jam’iyyar PDP ke da guda 10.

A jawabinsa bayan karbar shaidar lashe zaben, Aliyu ya bukaci jam’iyyun siyasar jihar su hada hannu da shi wajen sake gina jihar da kuma dawo da martabarta.

“Wannan nasarar ba tawa ba ce ni kadai, ta dukkanin mutanen Sakkwato ne da suka nemi canji.

“Don haka ina bukatar ‘yan jam’iyyun adawa da su zo mu hada hannu wajen sake gina jihar nan. Mu sake dawo da darajar jiharmu baki daya.”

Tun da farko, kwamishinan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), mai kula da jihohin Sakkwato, Kebbi da Zamfara, Farfesa Muhammad Sani Kalla, ya ce zabe ya zo ya wuce kuma al’ummar jihar zabi abin da ran su ke so.

A cewarsa, abun a yaba ne kan yadda masu ruwa da tsaki suka taka rawar gani a lokacin gudanar da zaben.

Ya kuma yi addu’ar Allah Ya shiryar da wadanda aka zaba a kan tafarki madaidaici, ya kuma sa gwamnatinsu ta kasance mai amfani ga daukacin al’ummar jihar da ma kasa baki daya.

Shi ma da yake jawabi, shugaban jam’iyyar APC na jihar, Isa Sadiq Achida, ya yi kira ga jam’iyyun adawa, musamman PDP da su mara wa zababben gwamnan baya bisa yarjejeniyar da suka kulla a baya.