Fatan alheri ga Aminiya, yau wasikarmu za ta maida hankali ne kan ‘yan jaridar Internet, masu rubibin wallafa labaran karya na hotuna da na bidiyo. Abin haushi da takaicin shi ne mutane ba su tsayawa su tantance labari, kawai sai su rubuta a shafukansu, domin neman mabiya, wasu kuma burinsu shi ne a ce su ne suka fara ba da labarin kuma akasarin labaran na karya ne. Alal misali, a karshen makon nan an kai wani hari a garin Damaturu, cikin mintuna talatin kacal da fara harin, sai ga wani faifan bidiyo yana ta yawo a intanet da nufin cewa shi ne abin da yake faruwa a Damaturun kuma da masana suka yi binciken wannan bidiyo, na wani shirin fim ne aka yanke aka sanya kawai domin a tayar wa mutane hankali. To wai shin mece ce ribarka idan ka wallafa labarin karya a shafinka? Shin ko ka san adadin mutanen da za su ga labarin? Yaya Mutuncinka zai kasance a wurin wanda ya ga labarin daga gare ka kuma daga baya ya gano cewa ba gaskiya ba ne ? Saboda haka ya kamata mu hada karfi da karfe mu tsaftace yanar gizo, ta hanyar yaki da kalaman batanci da labaran karya.
Daga Idriss M Idriss Damaturu Jihar Yobe 08033775767
Sakin Kanal Sambo Dasuki
Assalamu alaikum Editan AMINIYA, ka ba ni dama domin in bayyana ra’ayina kan Gwamnatin Tararyar Najeriya a kan bayar da umarnin da ta yi kan sakin tsohon mai bai wa Shugaban Kasa shawara, Kanar Sambo Dasuki. Wannan ya yi daidai kuma abin a yaba ne, muna fatan gwamnati za ta rika bin doka da oda kamar yadda kotuna da dama suka ba da umarnin sakinsa amma gwamnati ta ki sakinsa, har sai da ya kwashe kimanin shekara hudu a ajiye a hannun gwamnati. Da fatan za a rika mutunta umarnin kotu.
Daga Arbiyyu Muhammad, Jihar Sakkwato Najeriya, 07050262109
Wutar lantarki ta leko ta koma a Albasu
Assalamu Alaikum, ina so wannan kafa mai albarka ta isar mana da kokon bararmu ga mai girma Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Badaru Abubakar Talamiz, domin kuwa tun a shekarar 2007 ne aka kai wa garina na Albasu tiransifoma, amma har yanzu ba labarin zuwan wutar lantarki a garin na mazabar Albasu Karamar hukumar Suletankarkar Jihar Jigawa a Najeriya. Allah Ya sa a dubi wannan kudiri namu.
Daga Mustapha Auwalu Albasu, 08075659534.
Allah wadai da harin Biu
Assalam Aminiya. Harin da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kai a garin Biu na Jihar Borno abin bakin ciki ne da takaici. Ya Allah Ka shiga tsakanin nagari da mugu a duniya baki daya kuma Ka tsare bayinka.
Daga Alh Umar Foreber Gashuwa. 08108003333.
Fatan alheri ga AMINIYA
Assalamu Alaikum Edita, da fatan kana lafiya da daukacin ma’aikatan jaridar AMINIYA. Muna maku fatan alheri, mun gamsu da ayyukkanku, muna tare da ku kowane mako kuma duk mako nakan saya, in na karanta nakan aje saboda tarihi da masoyinku.
Daga Abdulkadir Madaro Jihar Zamfara, 09038657194.
Jinjina ga jami’an ‘yan sandan Kano
Salam Editan jaridar Aminiya. Don Allah ina so a mika min sakon jinjina ga jami’an ‘yan sandan Jihar Kano a kan namijin kokarin da suke yi na tabbatar da tsaro a jihar da ma kasa baki daya kamar yadda suka ceto wasu yara da kabilar lbo suka sata suka canza musu rayuwa. Duk wanda yajagoranta aka ceto wadannan yaran, Allah Ya saka da alheri, sannan ina kira ga gwamnati da ta dau matakin hukunta duk wani mai hannu a ciki, sannan ina yi wa iyayen yaran murnar dawowar yaransu gida a cikin koshin lafiya.
Daga Sulaiman Muhammad Masanawa Kabo Jihar Kano, 09012961055.
Kira ga Dan Majalisar Dawakin Tofa /Rimin Gado
Assalamu alaikum Edita, don Allah a ba ni dama in isar da sakona ga Dan Majalissarmu na Tarayya, Tijjani Abdulkadir Jobe mai wakiltar Dawakin Tofa, Rimin Gado da Tofa. Wannan ne zangon mulkinsa na hudu, amma mutum daya tak ya taba sama wa aikin soja a kan ya ji tsoron Allah, ya sani, wallahi Allah zai tambaye shi ranar kiyama a kan hakkinmu.
Daga Abubakar Kabir Lambu K/H Tofa Kano, 08149437671.
Murnar cikar Kwankwaso 63
Salam Edita, don Allah ka ba ni dama na taya tsohon Gwamnan Kano kuma tsohon Minista kuma tsohon Sanata Injiniya Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, murnar cikarsa shekara 63 a duniya. Ina masa fatan Allah Ya kara wa rayuwarsa albarka.
Daga A. B. Abubakar Lambu, 08149437671.
Kira ga Gwamnan Sakkwato
Assalamu alaikum Edita, da fatan kana lafiya. Ina kira ga Gwamnan Jihar Sakkwato da ya yi bincike game da abin da ke faruwa a Karamar Hukumar Gada. Saboda ba a biyanka albashi idan kai ba dan jam’iyyar PDP ba ne. Idan kuma shi ya ba su umarni mu sani. Kuma ya yi bincike a kan makarantun firamare na kauyukan Gada musamman garin Dukamaje da Gidan Albakari da Gidan Kuka. Saboda duk wadannan makarantu akwai malamai a rubuce, amma ba s|u zuwa saboda suna da daurin gindi. Mun kai korafi an ki a duba. Muna fatan mai girma zai yi bincike.
Daga Bashar Garbati Dukamaje, 08167791483.
Keta hakkin almajirai
Yanzu wannan wulakanci da ake yi wa malamai da sunan wai suna keta hakkin almajirai, gwamnati ba ta san kunya ba, yanzu ka je sel-sel na ‘yan sanda ka ga yadda ake cin zarafin mutane a turakunan sel. Kuma da yawa hatta bahaya nan za ka yi a cikin kanta suna kallonka kuma ko kwana nawa za ka yi ba su bari ka yi Sallah ko a kan bashi ne haka za a yi maka, amma wai ‘yan sanda sun dawo wai suna kai farmaki makarantun allo, wai ana cin zarafin yara.
Daga Sani Jihar Kebbi, 07032922021.
Sakon ta’aziyar mu
Assalam jarida mai farin jini ta Aminiya, ku mika mana sakon ta’aziyyarmu ga kungiyar zabi sonka reshen Jihar Gombe, bisa rasuwar daya daga cikin mambobinta Hussaini Almusaya Gombe.
Daga 08130446601.
Tunatarwa ga talakawan Najeriya
Edita, ina fadawa talakawa ‘yan uwana kusa mafita saboda ra’ayina ba irin naka ba, kila muna da bambancin ra’ayi, abin da zai amfani kasata, al‘umar kasata banda wata kasa da tafi Najeriya, ko ina naje ni dan kasar nan ne Najeriya. ‘Yan uwa mu tausayawa junanmu mu gina kasarmu da zuciya daya, mu zamanto a dunkule kunga in mubi tafarkin nan mun huta, kuma ga siyasa duk da iskar dimukuradiya muke ciki mu baiyanawa shugabanninmu kokenmu.
Daga 07034542318.
Kira ga Gwamna Masari
Assalamu alaikum da fatan kuna cikin koshin lafiya, Allah Ya sa albarka. Ina mika gaisuwa ga Gwamna Masari, muna cikin wani yanayi a kawo mana dauki muna cikin wani hali a nan Legas, an kama mutananmu ba su ji ba ba su gani ba. A taimaka masu.
Daga Yusuf Salisu Kankiya 09012318428.
Allah Ya kawo mana zaman lafiya
Assalam Edita, ina fatan kana lafiya Allah Ya karawa ilimi albarka, Don Allah ina so ka ba ni dama nayi kira ga al’ummar kasarmu Najeriya ba muda wata kasa da tafi mana ita, kasarmu tana bukatar addu’a, mu yawaita addu’a akan Allah Ubangiji ya kawo mana zaman lafiya mai dorewa, a maimakon zagin shugabanni da aibantasu, Allah Ya kuma Sanya albarka a abin da muka noma amin.
Daga Haladu Ahmadu Chibiyayi Zaki Jihar Bauchi. 08030703952.
Bayar da cin hanci don samun aiki
Asalam alaikum Aminiya Allah Ya kare wannan gidan jarida da kuma kasata, sakona zuwa ga shuwagabanni kowa da kowa saboda kura da shan bugu gardi da kwace kudi, mu yi addu’a mu tsaya ko zamu mutu, sai ku amma da kun shige mun zama banzaye kenan ku samu mu yita zarya a kafa muna fama, amma a banza da kun rabu da mu sai a jefar to mu yanzu an gama yi mana dadin baki. Khaki in har Allah Ya sa za mu sa to ba wanda ya isa ya hana saboda mu mun ba da rayuwarmu ga kasarmu ko yau ko gobe, koyaushe, Allah Ya ga zuciyar mai son yi, wadanda ake ba cin hanci suke cire sunanmu to su sa sunan mai kudi Allah Ya fi su kuma akwai ranar da Ubangiji zai ce mu ne to ranar fa ba mulki ba kudi kuma wadanda suka yi ma hanyar aikin khakin ba za su taimake su da komai ba.
Daga Aminu Haruna Ahmad Kankiya, 07068243769.
Son zuciya a harkokin siyasar Najeriya
Assalam Edita, ina so ka ba ni dama domin in fadi ra’ayina a kan harkokin siyasar kasar nan, masamman irin yadda son zuciya da jahilci yake taka rawa a fagen siyasa. Mene ne shugabannin APC ba su yi na zalunci a yanzu? An kama gwamnoni da satar kudin al‘umma an kama Ministoci da satar kudin jama’a duk a APC, amma saboda jahilci da son rai duk wannan ba laifi ba ne saboda suna jam’iyyar Buhari, duk abin da suka yi daidai ne.
Daga Hadi Tsohon Sarki Daura-07015256836
Ga masu yada jita-jita
Edita, don girman Allah ba ni fili in yi kira ga ‘yan Najeriya ta Arewa kan mu ji tsoron Allah, mu guji karya, sharri, gulma da kage, mu guji yada jita-jita da furta kalamai barkatai marasa sahihanci, mu daina fadin labarai marasa tushe bare ma mu kama, mu rika tabbatar da sahihancin labari kafin mu fada wa wani kuma mu daina saurin yarda da labarin da ba mu da ingancin gaskiya kansa, mu daina yarda da labarin kanzon kurege ko wane-ya-ga-wane.
Daga AmiRu Isah Bakori, 07068147933.
Sakon godiya ta musamman
Assalam Edita, Ina so ka ba ni dama domin in kara yin godiya ga Hon Aminu Jamu Daura, saboda irin abin arzikin da Aminu Jamu, ya yi mini shi ne mutum na biyu a duniya wanda har in koma ga Allah bazan taba mantawa da suba na farko tsohon shugaban hukumar ilimin baidaya na jihar Katsina Alhaji Aminu Dan Baba Khadimul Islam na masarautar Daura, wanda shi ne ya daukeni aikin gwamnati sai Alhaji Aminu Jamu, wanda ya biya mini makudan kudi aka yi mini tiyata a asibitin Bawo Clinic Daura, dan haka ina fatan Allah Ya kara kare shi daga sharrin abokan halitta mutum ko aljan amin.
Daga Hadi Tsohon Sarki Daura-07015256836-08164205067.
Kira ga Gwamnatin Kano
Assalam Edita, da fatan kana lafiya, tabbas kauyukan Karamar Hukumar Tofa na cikin (Lahaula) ba hanya ba ruwa ba wuta, ba wani aikin ci gaban da ake mana. Daga Y. Yarimawa, 08056333326.
Kwankwaso: Taya murnan cika shekara 63
Assalam AMINIYA ya aiki? Ina mika sakon taya murnan cika shekara 63 ga mai girma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, baya goya marayu, jigon talakawa, sannan muna na yi wa Abba Gida Gida, ina fatan Allah Ya yi wa rayuwa albarka tare da kara nisan kwana. Daga Aisha Muhammad Gombe. 07087675948.
Jinjina ga Gwamnan Zamfara
Assalamu alaikum Edita, da fatan kuna cikin koshin lafiya ku ba ni dama in yabo ga gwamnatin Jahar Zamfara Alhaji Bello Muhammad Matawallan Maradu, dangane da karshen matsalar tsaro da ya kawo wanda ta’addabi jahar baki daya Allah Ya sakamashi da alherinsa, amin Allah Ya kara kawo karshe matsalar tsaro a kasarnan baki daya, Allah Ya kare mu daga sharrin masu sheri baki daya Allah Ya kara muna imani da tsoran Allah da sunan Annabinsa Muhammadu Rasulillahi S A W. Daga Muhammadu Musa Mai Haki Gusau Sabuwarkasowa, 07067887164.
Hadarin mota: Sakon ta’aziyya
Assalam Edita, Ya Allah muna tawasali da tsarkaken sunayenka 99 Kajikan wadanda suka riga mu gidan gaskiya sakamakon hadarin mota Agozaki na jahar Bauchi Allah Ya sa jannatul fiddausi ne makomarsu amen. Zuwa ga fadar gwamnatin Bauchi a tarayyar Najeriya wasalam abu yazyd loko, 08075859580.
Jinjina ga Sanata Kabiru Gaya
Edita taimaka mini in jinjinawa Kabiru Gaya, da ya yi dogon tunani daya hango daya daga cikin matsalolin kasar nan. Aikinka ya yi kyau Sanata Gaya. Ni da ina dar-dar dakai, to amma gaskiya yanzu ka birge ni dari bisa dari saboda yinkurin ka na rage jam’iyyu su koma biyar kacal. Duk mai son dimokaradiyya da kasar nan zai so haka. Wani hanzari ba gudu ba shi ne a kara ragewa yawan ‘yan majalisu da na Dattawa, tarayya da jihohi saboda suke zuke kuda den da ta kamata a yi wa kasa aiki. Daga Lawan Yaro Bichi Yandadi Kunchi, 09023326156.
Dokar sakin aure a Kano
Assalam Edita, mun karanta bayani a cikin AMINIYA za a yi doka akan sakin aure a Kano idan mu maza muna da laifi to yaza a yi da matan dake neman sai an basu saki, a yanzu haka matata ta tafi Makkah neman kudi ita da wakilanta shekara 10 tana can menene mafita. Daga Naku A Abdul Jigawa, 08134540157.
Idan an saki ‘yan mari to za a iya sakin fursunoni
Assalam Edita, ka ba ni dama in yi tsokaci kan sakin ‘yan mari da ake yi, hakan ba zai haifar da da me ido ba, domin kuwa duk wanda ka gani a wurin saboda ya gagari iyayensa ne yasa aka daure shi, ba na gari bane, kuma acan ana kula da tarbiyyar su gami da addinin su haka suna karatun al’kur’ani, yanzu masu laifi za su karu tabbas barna zata karu, gyara ya kamata a yi akan hakan, kamar abincin su da wurin kwanan su da tsaftar muhallin su game da kula da lafiyarsu, shi ne mafita amma ba sakin su ba. Daga Raheenat Kofar Mazugal Kano, 09038967985.
Tunatarwa ga Ganduje da Kwankwaso
Assalamu alaikum Edita. Ina son ka ba ni dama in roki Gwamnan Kano Ganduje da tsohon Gwamna Kwakwaso don Allah don Annabi Muhammadu ku daina kai ‘yan uwanmu musulmi suna kashe kansu kuna bata mana sunan Arewa. Malam Sanda Dan Zariya Kasuwan Mil12 Lagos, 08101619017.
Jinjina ga Adam A Zango
Assalam Editan, jinjina zuwa ga Adam A Zango, kamar yadda ka dauki nauyin karatun daliban makarantar nan, kaima Ubangiji Allah Ya taima keka ya kare ka. Daga 08039258288.
Matashi mai kishin talaka
Assalam Edita. dan Allah ka ba ni dama in yaba wa matashin nan mai kishin talaka wato Bashir Sanata dan Jam’iyyar PDP a Jahar Kano, kuma dan amanar Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, bisa yadda yake ba dare ba rana dan ganin an tallafawa talaka kuma an hada kai ako ina dan a samu ci gaba da fatan Allah Ya kara jagora ya baka ikon ci gaba da fadin gaskiya ya kuma kawo babar kujera amen. Daga Musa G G C Kurna Kano, 08038822292.
Tunatarwa: Talakawa ‘yan Arewa
Edita sannun ku da aiki, so nake ka ba ni fili naja hankalin talakawa ‘yan uwana ‘yan Arewa, musamman mu Arewa gaba dayan mu a yanzu dan Arewan yake mulkar kasar nan, sai gashi wasu na Arewa na cewa bai tsinanawa Arewar komi ba, harda cewa takawan Arewa suka zabe shi sukan goranta masa to tabbas talakawa suka dora shi kan mulkin Najeriya amma bada son zukatan ku ba kuma fadar hakan ruwa ne ya karewa dan kada, wahalar da kuka baiwa talakawa shi ne tushe samun mulkin shi Buhari, talakawa sun ga mafita suka waste muku. Gaskiya dai daci gare ta mai fadarta bashi da farin jini ga makaryaci. Daga Ibrahim Dankoli Jada Adamawa, 07034542318.
Gyaran hanya
Salam Editan Aminiya, ina son ka bani fili a jaridar nan, kamar yanda Auwalu Datti ya yi jinjina ga kwamashinan aiyyuka da gidaje Aminu Usman P A, muna so kamar yanda aka dauko aikin titi daga kofar gidan Sardaunan Gumel zuwa Balai Kofar Auwalu Garba muna so ta zarce zuwa layin Gidan Magaji Maye, har kan babban titi Hadeja. Da fatan za a taimaka. Daga Rabiu A Usman Mailu Zuwan Wanki Gumel 07034852558.
Najeriya tana bukatar addu’a mu yawaita addu’a
Assalam Edita, ina fatan kana lafiya Allah Ya karawa iliminka albarka, don Allah ina so ka ba ni dama nayi kira ga al’ummar kasar mu Najeriya ba mu da wata kasa da tafi mana ita, kasar mu tana bukatar addu’a, mu yawaita addu’a akan Allah Ubangiji ya kawo mana zaman lafiya mai dorewa, a maimakon zagin shugabanni da aibanta su, Allah Ya kuma Sanya albarka a abin da muka noma amin. Daga Haladu Ahmadu Chibiyayi Zaki Jihar Bauchi. 08030703952.
Bude kasuwar garin Geidam
Assalam Edita, don Allah mu al’ummar garin Geidam ka mika mana gaisuwar mu da godiya ta musamman, zuwa ga gwamnan Jihar Yobe game da wannan goma ta arziki da ya yi mana na bude kasuwa. Daga Abdullahi Adamu Tsangayar Kashi, 09076468540.
Ciwon Mayawuya
Edita, muna son ku taimakamana akwai ciwo da a yanzu yake damun mutane wato ciwon mayawuya. Muna bukatar a taimaka mana. Ko zamu samu masu maganinta, da fatan ALLAH Zaisa mu dace. AMIN AMIN. Daga Sadi Danga, 08060775533.
Hana shigowa da shinkafar waje
Salam, Edita game da hana shigowa da shinkafa Najeriya, alhali abincin bai wadaci ‘yan Najeriya ba, me hanawar ai shi ba manomi bane, in kuma ance manomi ne to a ina gonarsa take? Me yake nomawa? Daga Abdurahman Mai Agogo Hadejia, 08033836968.
Matsalar sace wayar wutar lantarki
Assalamu Alaikum. Muna kira ga shugabannin siyasa na karamar hukumar Akko ta jihar Gombe da su duba matsalar sace wayar wutar lantarki da aka yi a daya daga Turansfomomin wuta na Tumu wanda ya haddasa yanzu wani sashen garin ba wutan lantarki. A kawo mana dauki dan Allah. Daga Isa Usman Tumu. 07060563008.
Kira ga Hukumar Ilmi ta jihar Kano
Dan Allah me hukumar ilimi take nufi da sanya farin unifoam a makaranatar gwamnatin jihar tun a firamare zuwa Sakandare abin da ke wahalar da iyayenmu wajen wanki sabanin sauran birane tun a firamare zaka gansu abin sha’awa misali: idan kaje jihar Kaduna bakinka ba zai rufu ba dan sha’awar dalibai zasu baka ganin kure hange zaka yi tayi ba tare da gajiya ba a makarantunsu. Daga Hafiz Na Maaiki Gwarzo, 08140900999.