Sha’anin rigingimun siyasa tsakanin bangaren Kwankwasiyya masu imani da wato mabiya tsohon Gwamann Jihar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da mabiya Gandujiyya wato magoya bayan Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje yana kara ta’azzara inda a kwanan nan aka ji Gwamnan ya yi wasu kalamai da suka tayar da kura a jihar.
Aminiya ta ruwaito daga wani faifan murya da ke yawo a kafafen watsa labarai inda aka ji Gwaman Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya barranta kansa da Kwankwasiyya tare da daukar alwashin ba zai taba yin sulhu da Kwankwasiyya ba. “Wai ‘yan Kwankwasiyya suna so a daidaita, wacce irin daidaitawa. To idan aka daidaita ya za mu yi da sanya jar hula? Sai mu dawo mu ce kowa sai ya sa jar hula ke nan?Mu da Kwankwasiyya haihata-haihata. Idan ba ka san Hausa ba ka je a fassara maka haihata-haihata.”
Gwamna Ganduje ya yi wadannan kalami ne a lokacin da yake bayyana takaicinsa game da daukar matakin shari’a da bangaren Kwankwasiyyar ya yi akan hana gudanar da zaben Qananan Hukumomi da ake sa ran gudanarwa a ranar Asabar mai zuwa.
Ganduje ya ce “Duk da irin tsare-tsaren da muka yi na gudanar da zabe amma wadannan mutane ‘yan Kwankwasiyya ba su dubi duk irin abubuwan da aka shirya wajen yin wannan zabe ba, sun kai mu kara a Abuja cewa a dakatar da zabe. Wadannan ka kira su masoya? Ban taba ganin kiyayay irin wanann ba, ban kuma taba ganin zagon kasa irin wanan ba, ban kuma taba ganin shashanci irin wannan ba. An je Abuja a fafata tsakanin lauyoyinmu guda bakwai karqashin jagoarancin Kwamishin Sharia na Jihar Kano su kuwa sun tafi da lauya guda daya mai I’I’ina”
Har ial yau Gwaman Ganduje ya yi hangen nasarar zaben ga bangarensu na Gandujiyya inda ya ce “ Ranar Asabar zuwa magariba an kammala zabe ku kan ku kun koma gidajenku”
Har ila yau Ganduje ya karyata kurarin da ya ce Kwankwasiyya na yi cewa matukar ba a daidaita tsakaninsu da Gandujiyya ba , to Ganduje ba zai ci zabe ba, inda ya bayyana hakan a matsayin karya da tatsuniya.