✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

MTN ya kasa cimma yarjejeniya da NCC

Hukumar da ke sa ido a kan kamfanonin sadarwa a kasar nan (NCC) ta ki amincewa da ragin kashi 80 cikin 100 na tarar da…

Hukumar da ke sa ido a kan kamfanonin sadarwa a kasar nan (NCC) ta ki amincewa da ragin kashi 80 cikin 100 na tarar da ta ci kamfanin sadarwa na MTN kimanin makonni uku da suka wuce.
Wani jami’in hukumar ya ce: “Ba zamu amince da bukatar da kamfanin MTN ya nema daga garemu ba, inda yake naman ragin kaso kashi 80 cikin 100 na tarar da muka kakaba masa.”
Kodayake, a ranar Lahadin da ta gabata ne MTN ya ce hukumomi sun tsawaita wa’adin da suka dibar masa domin ya biya tarar da aka sanya masa.
Hukumar ta sanya wa MTN tarar Dala biliyan biyar da miliyan 200 saboda ya kin rufe layukan mutanen da ba su yi rijista da shi ba har wa’adin yin rijistar ya wuce.
Hukumar ta bukaci MTN ya biya tarar ranar 16 ga watan Nuwamba wato (ranar Litinin da ta wuce).
Sai dai wata sanarwa da kamfanin ya fitar ta ce, “Muna sanar da masu hannun jari a cikin kamfanin cewa hukumomin Najeriya sun amince su tsawaita wa’adin da suka sanya mana domin mu biya tara har sai mun kammala tattaunawar da muke yi da su.”
MTN ya kara da cewa za su ci gaba da tattaunawa da hukumomin Najeriya kan rahin rufe layukan mutanen da kuma yadda za a shawo kan lamarin.