✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mourinho zai bar kulob din Real Madrid

A ranar Litinin da ta gabata ne shugaban kulob din Real Madrid Florentino Perez ya bayar da sanarwar kulob din zai raba-gari da kocinsa Jose…

A ranar Litinin da ta gabata ne shugaban kulob din Real Madrid Florentino Perez ya bayar da sanarwar kulob din zai raba-gari da kocinsa Jose Mourinho a karshen kakar wasa ta bana watau daga ranar 1 ga watan Yuni mai zuwa kenan. Shugaban kulob din ya ce kimanin shekara uku kenan da kocin yake horarwa kuma yana da sauran shekara uku a kwantaraginsa a halin yanzu amma duk da haka kulob din ya shiga yarjejeniyar raba-gari da shi ne saboda wasu dalilai.
Sai dai shugaban ya yaba wa Jose Mourinho a kan namijin kokarin da ya yi a shekara ukun da ya shafe a kulob din inda ya lashe wasu kofuna da suka hada da kofin Sarki (Kings Cup) da kofin La-Liga da kuma kofin Super Cup.
Sai dai masana harkokin wasanni sun yi hasashen Mourinho ya samu matsala da kulob din Madrid a kakar wasa ta bana ne bayan ya kasa lashe manyan kofunan da ake ji da su a Sifen da kuma Nahiyar Turai.
Kulob din Borussia Dortmund da ke Jamus ce ta fitar da Madrid a gasar zakarun kulob-kulob na Turai a matakin kusa da na karshe (Semi Fainal) a watan jiya sannan a makon jiya kuma kulob din Atletico Madrid ya yi wa Madrid kancal wajen lashe kofin Sarki (Kings Cup) yayin da FC Barcelona ta daga kofin La-Liga da ta kwace daga Real a ranar Lahadin da ta wuce.
Wadannan dalilai suka tunzura mahukunta kulob din wajen yanke shawarar korar koci Jose Mourinho.
Rahotonni sun tabbatar kulob din ya yi yarjejeniya da Jose Mourinho ne wajen sallamarsa ganin yana da sauran shekara uku a kwantaraginsa.  Kenan kulob din zai biya Mourinho wasu kudi a matsayin tara tun da ya kore shi ne tun kafin wa’adin kwantaraginsa ta kare.
Tuni rade-radi suka yi nisa cewa Mourinho na shirin canza sheka zuwa tsohon kulob dinsa Chelsea da ke Ingila ne.  Sannan ana sa ran kocin Paris Saint Germain watau PSG da ke Faransa Carlo Ancelloti ne zai maye gurbinsa a kulob din Real Madrid.  Shi kuma kocin Chelsea Rafa Benitez ana tunanin zai koma kulob din PSG da ke Faransa don cigaba da horarwa.
Kafin Mourinho ya bar Madrid sai da ya yi takun saka da ’yan wasan kulob din irin su Iker Casillas da Sergio Ramos da Pepe da Cristiano Ronaldo da kuma mahukunta kulob din.

Katsina Sportlight ta sake samun lambar yabo

Daga Ahmed Kabir a Katsina

Kungiyar wasan kwallon kafa ta Katsina Sportlight ce kadai ta jera shekaru hudu tana samun lambar yabo a jere daga Hukumar wasan kwallo ta kasa watau NFA akan yadda take biyan hakkokin ‘yan wasa da suka hada da biyan albashinsu a kan kari da duk abubuwan da suka wajaba  a kan lokaci.
Haka kuma Hukumar ta yaba wa kungiyar kasancewa ita ce daya tilo a fadin kasar nan da basussuka ba su yi mata katutu ba.
Hakan  na daga cikin irin nasarorin da kungiyar ta samu daga irin gagarumin tallafin da gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Ibrahim Shema yake bai wa kungiyar.
Shugaban kungiyar ta Katsina Sportlight, Alhaji Ayuba Gambarawa ya shaidawa Aminiya wadannan bayanai a wata hira da suka yi a kwanakin baya. Ya kara da cewa a yanzu haka kungiyar na a matsayi na biyu daga cikin kulob 15 da suka fito daga Arewacin kasar nan a rukunin kwararru wadanda ake kira da furofeshinal (Professionals).
“Batun gasar cin kofin kalubale na jihar kuwa shekara hudu kenan muke lashe kofin wanda muke shirin zuwa gasa ta kasa wato Challenge Cup, kuma duk wadannan nasarori ba sa rasa nasaba da irin jajircewa daga wajen ‘yan wasa dahukumar gudanarwa da gwamnatin jiha da kuma magoya baya da suke bai wa kulob din”.
Kamar yadda Shugaban ya ce, suna samun nasarar wasannin da suke yi ta hanyar zama da duk wani jami’i da mai ruwa da tsaki a kungiyar don tattaunawa akan irin abubuwan da za su gabatar a duk lokaci da kuma bayan buga kowane irin wasa.
Alhaji Ayuba ya ce kungiyoyi biyu ne kadai suka fita waje a gasar lashe kofin zakarun kulob-kulob na Afirka a wannan shekara inda suka samo maki uku-uku wato Katsina Sportlight sai kuma DSS ta Kaduna duk kuwa da kasancewar akwai kungiyoyin da suke kallon kansu a matsayin manya. 
Ta fuskar matsaloli kuwa,Alhaji Ayuba ya nuna takaicinsa akan irin yadda har yanzu ake karancin masu saka jari a bangaren wasannin kwallon kafa.. “In ka debe da wasu kadan daga cikin jami’an gwamnatin jiha irin su Kwamishinan kula da harkokin wasanni na Jihar Katsina babu wani ko wasu kamfanoni masu zaman kansu da ke tallafawa harkar wasanni a jihar.
Daga nan ya jinjina wa gwamnan Jihar Katsina Barista Shehu Shema a kan irin hadin kai da goyon bayan da yake bai wa kulob din Katsina Sportligh kuma ya sha alwashin cigaba da daukaka martabar jihar a bangaren lashe manyan kofuna a ciki da wajen kasa.

Dabid Beckham zai sayi  kulob din kwallo a Amurka

A ranar Litinin da ta wuce ne wakilan shahararren tsohon dan kwallon Ingila da kulob din Manchester United Dabid Beckham suka fara cinikin wani kulob a Amurka da ake yunkurin kirkiroshi wanda zai rika wasa a gasar rukuni-rukuni ta kasa a madadinsa.
Rahotanni sun tabbatar wakilan sun isa Amurka ne don yin cinikin wani sabon kulob a madadin dan kwallon da ya yi ritaya a karshen makon jiya.
Shi dai Dabid Beckham ya koma Amurka ne a shekarar 2007 don cigaba da yin kwallo.  A kwantaragin da ya sanya wa kulob din LA Galady a wancan lokaci ya hada da ba shi dama ya mallaki kulob na kashin kansa a Amurka da zarar ya daina buga wasan kwallo. 
Don haka a wannan lokaci da Beckham ya daina kwallo ne ya yanke shawarar komawa Amurka don ya cika burinsa na mallakar kulob na kashin kansa.
Idan ba a manta ba a ranar Alhamis ta makon jiya ce Dabid Beckham ya bayar da sanarwar yin ritaya daga wasan kwallo bayan ya cika shekara 38.
Mataimakin shugaban Hukumar shirya wasan kwallo a Amurka Dan Countermanche ya tabbatar cewa tuni wakilan Beckham suka ziyarci Amurka don tattaunawa da hukumarsu akan batun mallakar sabon kulob a Amurka.
Kafar yada labarai ta BBC ta ruwaito a watan Disamban shekarar bara cewa tuni wasu jami’an kulob daban-daban har guda biyu da ke buga wasa a gasar rukuni ta Amurka suka tuntubi Beckham a kan yiwuwar mallakar daya daga cikinsu.
Gasar rukuni ta Amurka da ake wa lakabi da MLS dai tana da jerin kungiyoyin kwallon kafa guda 19 ne don haka take yunkurin kirkiro daya don su zama 20.  Rahoton ya ce akwai yiwuwar a kafa sabon kulob din ne a garin New York City.