✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mourinho ya nemi afuwar Salernitana

An kusa bai wa hammata iska tsakanin mataimakin Mourinho da kocin Salernitana.

Kocin AS Roma Jose Mourinho ya nemi afuwar kungiyar Salernitana, biyo bayan tsokana da kuma bakar maganar da mataimakinsa Salvatore Foti ya fada wa ’yan kungiyar.

Yayin karawarsu ranar Lahadi a gasar Serie A, Roma ta doke Salernitana ne da kwallaye 2-1, abinda ya sanya kungiyar ci gaba da zaman dabaro a karshen teburin gasar.

Bayan wasan ne kuma daya daga cikin masu taimaka wa Mourinho wajen horaswa, Salvatore Foti ya yi tattaki zuwa gaban kocin Salernitana Davide Nicola yana mai fada cewar saura kiris a yi fatali dasu daga gasar Serie A su koma ta B.

RFI ya ruwaito cewa hakan ce ta sanya kocin da ya sha kaye kokarin yi wa mataimakin na Mourinho kulli ko dukan tsuguna ka ci doya, inda aka yi gaggawar shiga tsakani.

Yanzu haka dai Salernitana maki 16 kacal gareta bayan buga wasanni 30 a gasar Serie A, abinda ya sa take matsayin ta karshe yayin da ya rage wasanni 8 a karkare kakar wasa ta bana.