Kocin Manchester United Jose Mourinho da kocin Newcastle United Rafeal Benitez na daga cikin koci-koci da suke fuskantar barazanar sallama idan ba su tabuka abin kirki a kakar wasa ta bana ba.
Mourinho wanda yake fuskantar barazana daga mahukuntan kulob din United bayan da aka fara kakar wasa ta bana, yanzu haka kulob din na tsakiyar teburin gasar Firimiya ce inda Liberpool ta ba shi tazarar maki 6 a wasanni hudu.
Shi ma kocin Newcastle Rafeal Benitez yana fuskantar irin wannan matsala daga mahukuntan kulob din, inda a kakar wasa ta bana kulob din ya fada cikin matsalar rashin samun nasara a wasanni hudu da ya yi. Kawo yanzu kulob din na daga cikin wadanda suke kasan tebur a gasar Firimiya ta Ingila.
Kamar yadda kafar watsa labarai ta Naij.com ta kalato a ranar Talatar da ta wuce, wadannan koc-koci suna sahun gaba a jerin wadanda ake ganin za a iya sallama kafin a kare kakar wasa ta bana.
Mourinho dai ya horar a kulob da dama da suka hada da Chelsea da Inter Milan da kuma Real Madrid, yayin da Benitez ya taba horar da kulob din Liberpool da Real Madrid da sauransu.