✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Motar giya ta fadi a kusa da ofishin Hisbah a Kano

Tuni dai hukumar ta daka wawa a kan kira-kiras na motar

A wani yanayi mai kama da kaya ya tsinke a gindin kaba, wata mota makare da giya ta fadi a dab da ofishin Hisbah na Karamar Hukumar Kumbotso da ke Panshekara a Jihar Kano.

Rahotanni sun ce lamarin dai ya faru ne a daidai lokacin da motar da ke dauke da motar kirar Hilux ta fada cikin wata kwata.

Hatsarin dai, wanda ya faru da daren ranar Talata, ya yi sanadiyyar jikkatar direban motar, wacce ba a kai ga tantance daga inda ta fito ba.

Tuni dai hukumar ta Hisbah ta daka wawa a kan motar inda ta yi awon gaba da kiras-kiras na giya.

Kakakin hukumar ta Hisbah, Lawan Ibrahim Fagge ya shaida wa Aminiya cewa yanzu haka jami’ansu na can suna kokarin debo ragowar giyar daga wajen da lamarin ya faru.

A cewarsa, “Dama jami’anmu na Karamar Hukumar sun shafe kusan kwana hudu suna hakon motar, sai yau Allah Ya yi ikonsa da kanta ta fadi a kusa da ofishinmu.

“Ana amfani da motar mai kirar Hilux, inda ake sojan gona da ita a matsayin ta jami’an tsaro wajen dakon giyar.

“Yanzu dai an kama ta, kuma dukkana kwalaben giyar an kawo su hedkwatar hukumarmu da ke Saharada,” inji kakakin.