✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Motar dakon gas ta yi bindiga a tsakiyar unguwa a Abuja

Kwatsam jama'a suka ga direban motar ya yi fakin a wurin, kuma ya sanar da mutane cewa su gudu.

Mazauna yankin Gwagwa da ke Abuja sun shiga cikin rudani da daren Juma’a sakamakon fashewar wata motar dakon iskar gas a cikin unguwarsu.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:30 na dare, kusa da wani wuri da ake kira mahadar ’yan sanda, da ke Gwagwa.

Wasu shaidun gani da ido da suka zanta da Aminiya a daren Juma’a, sun ce kwatsam suka ga direban motar ya yi fakin a wurin, kuma ya sanar da mutane cewa su gudu.

Wani mazaunin garin mai suna Sani Khalid ya ce murfin da ke makale a daya daga cikin sundukan tankar ne ya fara ballewa, sannan gas din da motar ta dauko ya fara  yoyo.

“Cikin ’yan mintoci kadan motar ta kama wuta, wutar ta mamaye sararin samaniya, daga bisani kuma ta yi bindiga,” in ji Khalid.

Wutar da aka hango daga Kubuwa, mai nisan kilomita 20, ta shafe kusan awa guda babu mai iya zuwa kusa da inda take ci.

Ba a kai ga tantance yawan barnar da gobarar ta haddasa ba.