✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Motar da aka shekara 10 ana tara kuɗinta ta ƙone bayan awa 1 da sayen ta

Ya kwashe mintuna 20 yana kallon burinsa ta ƙone kusan gaba ɗaya.

Bayan da wani matashi ɗan shekara 33 ɗan kasar Japan mai suna Honkon ya yi tarin kuɗi na tsawon shekaru 10 don siyan motar da yake mafarki — na wata sabuwar mota ƙirar Ferrari 458 Spider — sai ya zauna yana kallon yadda motar take ƙonewa cikin sa’a ɗaya da tuƙa ta a karon farko.

Kafofin sada zumunta na ƙasar Japan sun yi sharhi game da rahoton baƙin ciki na Honkon, matashin da ya kasance mai shirya wakoki, wanda ya kashe makudan kuɗi game da mafarkin sayan motarsa ta Ferrari, sai dai ya kalle ta tana ci da wuta a ranar da ya tuƙa ta a karon farko.

Dan shekara 33 kwanan nan ya dauki hankalin mabiya manhajar X (Twitter) don yaɗa labarin kan yadda zai ji daɗin gaskata mafarkin mallakar Ferrari a ’yan mintuna kaɗan kawai ta kama da wuta yayin da yake tuƙi a kan babbar titin Shuto a Tokyo, Laraba, 16 ga Afrilu.

A bayyane yake, an kawo masa zabinsa Spider 458 ne kawai, kuma yana cikin motar kan gwaji tare da shi lokacin da ya lura da fitar wani farin hayaki.

Da farko ya ɗauka hayakin daga motar da ke kusa da tasa motar yake fita, amma yayin da motar ta yi gaba, sai ga shi hayakin yana fitowa daga cikin motar Ferrari.

Don haka sai kawai Honkon ya janye, ya fita daga cikin motar, ya kira hukumar kashe gobara.

Ya kwashe mintuna 20 yana kallon burinsa ta ƙone kusan gaba ɗaya.

“Ina tsammanin ni kadai ne mutum a Japan da ya taba fuskantar irin wannan matsala,” Honkon ya rubuta a shafin X, tare da taken hoton motar da ke konewa.

“Na kashe yen miliyan 43 kwatankwacin (Naira miliyan dari 4 da miliyan 92 dubu dari 283 da 620), kuma abin da na samu shi ne wannan hoton.”

Rundunar ’yan sandan birnin Tokyo ta sanar da cewa, babu alamun karo a jikin motar Honkon ta Ferrari, amma ana ci gaba da gudanar da bincike.

An yi imanin cewa gobarar ta tashi ne a cikin injin motar, amma har yanzu ba a san dalilin ba.

Yayin da a fili yake matashin ya yi bakin cikin rashin motarsa, Honkon ya shaida wa mabiyansa cewa ya yi farin ciki da ya rayu, domin yana tsoron cewa motar za ta iya fashewa yana ciki.