Mota ta take wani mai kwacen waya a lokacin yake kokarin tserewa bayan ya yi wa wata mata fashin wayarta a garin Kano.
Kakakin ’yan sandan jihar Kano, Haruna Abdullahi Kiyawa, ya ce mota ta take mai kwacen wayan ne a yayin da yake kokarin tsallaka titi bayan ya yi fashin.
A daren nan na Lahadi ne Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa, “Yanzu na samu rahoto daga Zoo Road wani ya zare Danbida ya kwaci wayar wata mata. Yana tsallaka titi mota ta take shi. Ana bukatar mu kaishi asibiti”
Kwacen waya na daga cikin matsalolin tsaro da suka addabi jihar Kano, inda a wasu lokuta masu kwacen ka hallaka jama’a.
- An cafke barayin janareton masallaci a Kaduna
- Abba ya nada Gawuna da Ganduje a Majalisar Dattawan Kano
A sanadiyyar wannan matsala, gomman mutane a jihar sun rasa rayuwarsu a hannun masu kwace waya, wasa da dama kuma suka tsallake rijiya da baya da rauni ko asarar dukiya.
Lamarin ya dan yi sauki baya-bayan nan a sakamakon matakan da ’yan sanda da gwamnatin jihar suka dauka.
A wata hira a aka yi da gwamnan jihar, Abba Kabir yusuf ya sanar da afuwa da kuma shirin tallafin sana’a ga ’yan daba, wadanda da akasarinsu ke harkar kwacen waya.