✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abba ya nada Gawuna da Ganduje a Majalisar Dattawan Kano

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nada babban abokin hamayyarsa a zaben 2023, Nasiru Yusuf Gawuna na Jami'yyar APC a Majalisar Dattawan Kano (KEC).

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nada babban abokin adawansa a zaben 2023, Nasiru Yusuf Gawuna na Jami’yyar APC a Majalisar Dattawan Kano (KEC).

Gwamna Abba ya kuma nada shugaban Jam’iyyar APC na Kasa kuma tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje, majalisar, wadda za ta zama zauren tattaunawa da kuma ba da shawara ga gwamnatin jihar.

Abba ya bayyana cewa tsoffin gwamnonin jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Sanata Ibrahim Shekarau su ma mambobi ne a majalisar.

Gwamnan Kanon ya bayyana cewa duk tsofaffin gwamnonin jihar da mataimakansu da sarakunan jihar mambobi ne a majalisar tuntubar.

Sauran ’yan majalisar sun hada da tsoffin shugabannin majalisar dattawa, da tsoffin shugabannin majalisar wakilai.

Haka zalika tsoffin shugabannin majalisar dokokin jihar da mataimakan, tsoffin alkalan kotun koli da na kotun daukaka kara da kuma tsoffin manyan alkalan jihar.

Sannan akawi manyan malamai, ’yan kasuwa, da tsoffin shugabannin hukumomin tsaro da wasu fitattun mutane.

Akwai kuma sakatarorin gwamnatin jihar, da tsofaffin shugabannin ma’aikatan gwamnatin jihar.

Gwamnatin ta nanata kudurin sa na ci gaba da gudanar da shugabancibsa zai tafe ida kuma, ba tare da rufa-rufa ba, kuma daidai da zamani.