✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mota ta kashe sojoji 2 a Kaduna

Motar ta murkushe sojojin bayan sun fada wani rami da babur dinsu.

Sojoji biyu na Makarantar Horas da Dakarun Najeriya (NDA) sun rasa rayukansu bayan da wata motar kwashe shara ta murkushe su babur dinsu a Kaduna.

Lamarin, a cewar wani ganau, ya faru ne da sanyin safiyar ranar Talata a yankin Mando da ke Afaka a jihar.

Ya ce, “Sojojin bayan faduwa a kan babur din ne suka fada wani rami a kan hanyar, sai motar da ke binsu a baya ta murkushe su.

“Lamarin gaba daya ya faru cikin kankanin lokaci wanda hakan ya sa aka yi rashin sa’a babu wanda ya iya ceto sojojin.”

An ce an garzaya da sojojin zuwa asibitin Dakarun Najeriya na 44 inda aka tabbatar da mutuwarsu.

Jami’in hulda da jama’a na NDA, Manjo Bashir Jajira, bai amsa kiran da wakilinmu ya yi masa ba a kokarin jin ta bakinsa.