✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mohammed Barau ya zama sabon Sarkin Kontagora

Gwamnan Neja ya nada shi bayan takaddamar da ta biyo bayan zaben.

Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya sanar da nadin Alhaji Mohammed Barau a matsayin sabon Sarkin Kontagora.

Alhaji Mohammed Barau shi ne Sarkin Kontagora (Sarkin Sudan na Kontagora) na bakwai bayan rasuwar magabacinsa, Alhaji Sa’idu Namaska mai shekara 84.

Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautu na Jihar Neja, Emmanuel Umar, ya sanar cewa an zabi Alhaji Mohammed Barau ne bayan zaman da masu zabar sarki na Masarautar Kontagora suka gudanar a ranar 19 ga watan Satumba, kamar yadda doka ta tanadar.

Ya ce bayan zaben, wasu daga cikin ’yan takarar kujerar sarkin sun rubuta wa gwamnan takardar korafi cewa suna zargin an aikata ba daidai ba a yayin zaben sarkin.

Bayan haka ne gwamnan ya yi zama da masu zabar sarkin da Majalisar Sarakunan Jihar, wadanda suka tabbatar masa cewa an yi komai bisa ka’ida a shari’ance da kuma al’adance a wajen zaben da aka gudanar ba tare da wani katsalandan ba.

Emmanuel Umar ya ce bayan haka ne kuma Gwamna Abubakar Sani Bello ya tabbatar da zaben Alhaji Mohammed Barau a matsayin Sarkin Kontagora na Bakwai