Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya sanar da nadin Alhaji Mohammed Barau a matsayin sabon Sarkin Kontagora.
Alhaji Mohammed Barau shi ne Sarkin Kontagora (Sarkin Sudan na Kontagora) na bakwai bayan rasuwar magabacinsa, Alhaji Sa’idu Namaska mai shekara 84.
- Za a fara biyan daliban jami’a alawus din N75,000
- ’Yan bindida sun kashe mutum 10 a masallaci a Katsina
Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautu na Jihar Neja, Emmanuel Umar, ya sanar cewa an zabi Alhaji Mohammed Barau ne bayan zaman da masu zabar sarki na Masarautar Kontagora suka gudanar a ranar 19 ga watan Satumba, kamar yadda doka ta tanadar.
Ya ce bayan zaben, wasu daga cikin ’yan takarar kujerar sarkin sun rubuta wa gwamnan takardar korafi cewa suna zargin an aikata ba daidai ba a yayin zaben sarkin.
Bayan haka ne gwamnan ya yi zama da masu zabar sarkin da Majalisar Sarakunan Jihar, wadanda suka tabbatar masa cewa an yi komai bisa ka’ida a shari’ance da kuma al’adance a wajen zaben da aka gudanar ba tare da wani katsalandan ba.
Emmanuel Umar ya ce bayan haka ne kuma Gwamna Abubakar Sani Bello ya tabbatar da zaben Alhaji Mohammed Barau a matsayin Sarkin Kontagora na Bakwai.