Attajiri dan asalin kasar Masar Mohammed Al Fayed kuma wanda ya mallaki kulob din Fulham da ke gasar rukuni-rukuni ta Premier da ke Ingila a shekaranjiya Laraba ne ya bayar da sanarwar sanya kulob din a kasuwa.
Shi dai Mohammed Al Fayed ya sayi kulob din Fulham ne tun cikin shekarar 1997 kimanin shekara 16 da suka gabata amma yanzu yake neman cefanar da shi ga duk mai bukata, kamar yadda jaridar The Mirror ta kalato.
Rahoton ya ce akwai yiwuwar attajirin ya sayar da kulob din a tsakanin Fam miliyan 150 zuwa Fam miliyan 200.
Rahoton ya ce, attajirin ya yanke shawarar sayar da kulob din ne saboda rashin samun isasshen lokacin zama a Ingila a mafi yawan lokuta don zirga-zirgar da yake na hada-hadar kasuwancinsa a wasu kasashen duniya.
A shekarar bara ce Al Fayed ya tallafa wa kulob din Fulham da Fam miliyan 212 don rage basussukan da ake bin sa kuma hakan ta sa ’yan kasuwa da dama suka nuna sha’awar zuba jari a kulob din.
Kulob din Fulham na daya daga cikin kungiyoyin kwallon kafa 20 da ke fafatawa a gasar rukuni-rukuni ta Premier.
A kakar wasan da ta wuce kulob din ne na 12 daga cikin kungiyoyin da suka fafata.
Mohammed Al Fayed ya sanya kulob din Fulham a kasuwa
Attajiri dan asalin kasar Masar Mohammed Al Fayed kuma wanda ya mallaki kulob din Fulham da ke gasar rukuni-rukuni ta Premier da ke Ingila a…
