✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mohammed Abacha ya sake komawa PDP

Dan marigayi Shugaba Sani Abacha Alhaji Mohammed ya sake komawa Jam’iyyar PDP. Mohammed Abacha ya so tsayawa takarar Gwamnan Jihar Kano a karkashin tsohuwar Jam’iyyar…

Alhaji Mohammed AbachaDan marigayi Shugaba Sani Abacha Alhaji Mohammed ya sake komawa Jam’iyyar PDP. Mohammed Abacha ya so tsayawa takarar Gwamnan Jihar Kano a karkashin tsohuwar Jam’iyyar CPC, wadda yanzu ta narke a sabuwar Jam’iyyar APC a zaben 2011, amma bai samu nasara ba.
An daina jin duriyar Mohammed Abacha na tsawon lokaci, sai bayan da aka sako babban jami’in tsaron mahaifinsa Manjo Hamza Al-Mustapha, inda ya rika yi masa rakiya a tafiye-tafiyen da ya yi, ciki har da na makon jiya inda suka je Imo suka zauna da shugabannin kungiyoyin kabilu na yankuna da sunan hada kan matasan kasar nan.
Da yake magana a sakatariyar Jam’iyyar PDP ta kasa a Abuja Mohammed ya ce sai da ya yi tuntuba sosai da magoya bayansa da sauran ’ya’yan jam’iyyar kafin ya dawo PDP, inda ya ce ita ce jam’iyyar da ta fi dacewa da shi.
Ya bayyana PDP da jam’iyyar da ita kadai c eta kunshi dukkan jama’a daga sassan kasar nan ba tare da lura da addini da kabila ba.
Ya yi alkawarin tattaunawa kan batun wakilcinsa a jam’iyyar nan gaba, sai kuma batun yafe masa kuma zai tuntubi Gwamna Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso.
Ya ce Gwamna Kwankwaso ne jagoran jam’iyyar a Jiha Kano, inda ya ce bai koma PDP don karbe iko daga Gwamnan ba.
Mohammed Abacha wanda ya samu rakiyar magoya bayansa, ya gana da a asirce da shugabannin jam’iyyar ciki har da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na kasa; Uche Secondus kafin ya bayyana komawarsa jam’iyyar.
Da yake mayar da martani kan komawar Mohammed Abacha zuwa PDP, shugaban tsohuwar Jam’iyyar CPC na Jihar Kano, Dokta Mohammed Mahmood Ababakar ya ce dama ya ja baya daga jam’iyyar.
“Dama daga PDP ya zo jam’iyyyarmu CPC, wadda ta koma APC, kuma ya koma inda ya fito. A siyasa mutane suna neman abin da yake yi musu dadi ne. Wasu kan tsaya a jam’iyya daya komai dadi komai wahala domin kare wasu bukatunsu,” inji shi.