✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Miyetti Allah za ta iya kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga – Sarkin Musulmi 

Lokaci ya yi da ya kamata a kawo karshen matsalar nan.

Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya bayyana cewa Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah (MACBAN), na iya ba da gudunmawa wajen magance matsalar hare-haren ’yan bindiga a kasar nan.

Sarkin Musulmi, ya ce shugabancin MACBAN na iya taimaka wa wajen kawo karshen matsalar ‘yan bindiga da ke garkuwa da mutane a Najeriya.

Ya bayyana haka ne a lokacin rantsar da sabbin shugabannin kungiyar MACBAN a Babban Masallacin Kasa da ke Abuja.

A cewar sarkin: “Kowa ya san Fulani suna tashi daga wani waje zuwa wani. Suna zuwa ko’ina suna yin aure. Kuma mu masu son zaman lafiya ne.

“Amma ta yaya muka kai ga halin da muke ciki a yanzu, mun gano ‘ya’yanmu Fulani ne, amma ba dukkaninsu ne suka shiga harkar fashi da garkuwa da mutane ba.

“Idan muka gana da shugabannin wannan kungiya  za su tattauna yadda za a shawo kan lamarin, domin lokaci ya yi da ya kamata a kawo karshen matsalar nan.

“Sama da shekara 48 da kafuwar MACBAN, muna bukatar samun wasu sabbin abubuwa da sabbin dabaru a cikin kundin tsarin mulkinta.”

A baya-bayan nan dai ana alakanta Fulani makiyaya da yin garkuwa da mutane da aikata fashin daji a kasar nan.

Ana zargin Fulani makiyaya da kai hare-hare kan manoma tare da korar al’umma, da kuma kai hare-hare kan cibiyoyin addini a fadin kasar nan.

Ana kuma alakanta makiyaya masu dauke da makamai sun karbi biliyoyin kudi a matsayin kudin fansa daga iyalan mutanen da ake zargin suna sacewa.