Hukumar NDLEA mai Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi a Najeriya, ta sanar cewa daga shekarar 2018 zuwa yanzu, ta cafke mutum 2,119 ciki har da mata 102 da ake zargi da ta’ammali da miyagun kwayoyi a jihar Kano.
Kwamandan NDLEA na Jihar, Dokta Ibrahim Abdul ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin zayyana wa manema labarai nasarorin hukumar tun daga shekarar 2018 zuwa yanzu.
- Mun tsiyace, kasafin kudin da ake ware mana ya yi karanci — Majalisa
- Kano: Mata na neman rabuwa da miji saboda lalacinsa
Abdul ya ce daga cikin wannan adadin, kotu ta yanke hukunci a kan 205 daga cikin wadanda ake zargi.
“A tsawon wannan lokaci, hukumar ta samu nasarar damke kilo dubu 13.505 na kunshin miyagun kwayoyi daban-daban a sakamakon namijin kokarin da jam’ianmu suka yi.”
“Mun samu damar cafke kilo dubu 10 na tabar wiwi da kilo dubu 3.412 na wasu sunadarai masu gusar da hankali da kuma kilo 3.171 na hodar iblis.”
“A zamanin jagorancina ne hukumar ta samu nasarar yin mafi girman kamu na fiye da kilo biyu na hodar iblis a lokaci guda.”
A cewar Kwamandan na NDLEA, “hukumar ta kuma yi wa mutane 1,619 gyaran hali masu ta’ammali da miyagun kwayoyi sannan kuma da kone kilo dubu 28.167 na miyagun kwayoyi a tsakanin watan Nuwamban 2018 kawo yanzu.”
Haka kuma, a zamanina ne hukumar karon farko a tarihinta, ta gano tare da tarwatsa wasu gonaki biyu na tabar wiwi a unguwar Wailari da ke Karamar Hukumar Kumbutso ta Jihar Kano.”
“Mun kuma gano wata cibiyar samar da maganin tari na Kodin a Karamar Hukumar Nasarawa ta jihar.”
“A tsakanin wannan lokaci, Jihar Kano ta samu gagarumar nasara bayan da Ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da Miyagun Kwayoyi da Laifuka ya mayar da Jihar Kano zuwa mataki na daya daga na shida a alkaluman jihohin da suka fi ta’ammali da miyagun kwayoyi a kasar baki daya.
Kwamandan ya kuma yi bayanin yadda suka ceto wata ’yar Najeriya da ake shirin zartar wa da hukuncin kisa a kasar Saudiya, bayan da aka zarge ta da safarar miyagun kwayoyi a jakarta yayin da suka ziyarci kasar tare da mahaifiyarta da zummar yin aikin Umara.
Ya ce hukumar ta kubutar da matashiyar ce bayan da aka zurfafa bincike kuma a gano cewa wasu ma’aikatan filin jirgin sama ne suka sanya mata kwayar a jakarta.
A karshe, ya yaba wa Gwamnatin da Masaurautar Kano da kuma sauran shugabannin addinai da masu ruwa da tsaki dangane da fadin tashin da suke yi na goyon bayan ayyukan hukumar.
Haka kuma, ya yaba wa sabon shugaban Hukumar NDLEA, Birgediya-Janar Buba Marwa, wanda a cewarsa hukumar ta inganta ayyukanta cikin kankanin lokacin da ya karbi ragamarta.