✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Miyagu na shirin jefa Najeriya cikin damuwa – Buhari

Buhari ya ce tilas miyagun su fuskanci fushin hukuma

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya ce hare-haren da ake kai a wuraren ibada a ‘yan makonnin nan aikin wasu maketata ne masu neman jefa Najeriya cikin rikicin addini.

Buhari ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar kan hare-haren da aka kai a wuraren ibadar, kamar yadda mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya bayyana.

Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya  kan su rungumi, tare da nuna kulawa ga wadanda harin ya shafa, su da ‘yan uwansu.

Daga nan, ya bai wa ‘yan kasa tabbacin kamo maharan don su fuskanci hukunci daidai da laifin da suka aikata.

Ya ce, maharan ba za su cim ma nasarar raba kan al’ummar kasa ba.

Sanarwar ta ce, “Daga abin bakin cikin da ya faru a Owo makonni biyun da suka gabata, zuwa kashe-kashe da garkuwa da mutane da ya auku a Jihar Kaduna a karshen makon da ya gabata, a bayyane yake cewa maketata sun yi shirin jefa kasa cikin rikicin addini.

“Shugaba Muhammadu Buhari ya yi amannar cewa addinanmu da bambance-bambancenmu, su ne suka daukaka Najeriya suke kuma karfafa ta shi ya sa makiya ke neman ruguza hakan ta hanyar haddasa fitina a tsakani.

“Ba za mu kyale su ba. Ba za mu bari wasu gurbatattu su raba hankalin kasa don manufofin siyasa ba.

“Maharan dabbobi ne, masu rauni kuma maketata, da suka bi suna karkashe mata da yara a wuraren ibada.”

Shugaban ya ce tilas miyagun su fuskanci fushin hukuma, tare da bai wa ‘yan kasa tabbacin hadaddiyar rundunar jami’an tsaro za ta taimaka wajen kamo batagarin.

Daga nan, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da zama al’umma daya da marataba juna don nuna wa miyagun cewa ba za su taba yin nasara a kan Najeriya ba.