A ranar 5 ga Fabrairun nan ne, ayarin Gwamnatin Tarayya a karkashin jagorancin Ministan Watsa Labarai, Alhaji Lai Muhammed da wadansu ministoci hudu ya ziyarci garin Maiduguri, fadar Jihar Borno domin taro na musamman na ganawa da jama’a a kan sojoji da tsaro. Taron shi ne irinsa na biyu da aka gudanar, bayan na farko da aka gudanar a Kano. Ministan Watsa Labaran ya bayyana wa Gwamnan Jihar Borno, Alhaji Kashim Shettima cewa ayarin ya zo Borno ne da nufin gane wa idonsu hakikanin ayyukan da sojoji da sauran hukumomin tsaro suke gudanarwa game da yaki da ta’addanci da kuma nufin nanata shirin Gwamnatin Tarayya na dawo da zaman lafiya a yankin. “Mun kuma zo nan Borno ne da nufin karfafa wa zakakuran sojojinmu, saboda sadaukar da rayukansu domin ganin Najeriya ta zama wurin zama mai dadi ga dukanmu.”
Gwamna Shettima ya yi maraba da ayarin, inda ya ce a cikin makonni shida da suka gabata, sojoji sun samu gagarumar nasarar da ba a samun irinta ba a cikin shekara uku da suka gabata. Zuwa lokacin hada wannan rahoton taron ganawar da ya kunshi ministocin tsaro da na al’amuran cikin gida da na kasafin kudi da tsare-tsare a matsayin masu kula da shi yana ci gaba da gudana. Taron ya samu halartar bakin da aka gayyata daga jihohin Adamawa da Borno da Yobe.