Ministar Harkokin Wajen Jamus Annalena Baerbock ta soma ziyarar aiki a kasashen Mali da Jamhuriyar Nijar da ke yankin Yammacin Afirka.
A birnin Bamakon na Mali Baerbock za ta gana da Assimi Goïta, shugaban gwamnatin mulkin soja ta wucin gadi da Ministan Harkokin Wajen Kasar, Abdoulaye Diop.
- Ministan Abuja ya kira taron gaggawa saboda matsalar tsaro
- Barcelona za ta iya lashe La Ligar bana —Ronaldinho
Gidan Rediyon Jamus ya ruwaito cewa daga nan za ta gana da wakilan Tarayyar Turai kan sojojin Jamus kimanin 300 da ke ba da horo a kasar ta Mali mai fama da tashe-tahsen hankula.
A birnin Yamai fadar gwamnatin Jamhuriyar Nijar, ministar za ta gana da Shugaba Mohamed Bazoum da ministan harkokin wajen kasar Hassoumi Massoudou inda za a tattauna kan batun dakarun Jamus da ke yankin sannan za ta gana da wakilan kungiyoyin fararen hula a duk kasashen biyu.
Yankin dai na fama da karin karancin abinci bayan kutsen da Rasha ta kaddamar a kan Ukraine.