✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ministan Shari’a ya auri ’yar Buhari a matsayin matarsa ta uku

Da yi wa Ministan tayin Hadiza har aka yi auren ko wata guda ba a dauka ba.

Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya auri ’yar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a matsayin matarsa ta uku.

Wata majiya ta shaida wa jaridar TheCable cewa, an daura auren Malami da Nana Hadiza a sirrance ne a ranar Juma’a a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Binciken Aminiya ya samu tabbacin cewa, Buharin ne ya yi wa Ministan tayin auren ’yarsa kuma ya amince saboda alaka ta kut-da-kut da ke tsakaninsu da ta samo asali tun kafin zuwansu gwamnati.

Wata majiyar mai kusanci da iyalan Buhari ta shaida wa Aminiya cewa, “Da yi wa Ministan tayin Hadiza har aka yi auren ko wata guda ba a dauka ba.

“An yi auren kuma yanzu haka har an kai ta dakin miji; tana nan a Birnin Kebbi.”

Nana Hadiza, mai shekara 41, ita ce ’yar Buhari ta uku tare da matarsa ​​ta farko, Safinatu wacce ya sawwake mata a shekarar 1988 kuma daga bisani ajali ya katse mata hanzari bayan ’yar gajeruwar jinya.

Nana Hadiza ta auri Abdulrahman Mamman Kurfi wanda ta haifi ’ya’ya shida kafin rabuwarsu da shi.

Da wannan auren, Hadiza ta zama matar Malami ta uku, bayan Aisha da Fatima.

An nada Malami a matsayin Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a ne bayan Shugaba Buhari ya ci zabe a shekarar 2015 – ya kuma sake nada shi mukamin a ranar 21 ga Agusta, 2019.