Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva, ya shiga sahun masu neman takarar kujerar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar APC mai mulki a kasar.
Wata kungiyar magoya bayansa mai suna ‘Good People of Nigeria’ ce ta sayi fom din neman takarar a madadin ministan.
- Jonathan ya fito takarar Shugaban Kasa a APC
- Shugaban Majalisar Dattawa ya shiga jerin masu neman takarar shugaban kasa a APC
Da take jawabi a gaban Babban Ofishin Kamfanin Man Fetur na Najeriya NNPC da ke Abuja, kungiyar ta ce ta saya wa tsohon gwamnan na Jihar Bayelsa fom din takarar ne duba da kwazonsa a Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur ta kasar.
Jagoran kungiyar, Alhaji Mohammed Abu, ya ce hakan ne ya sanya suka ga cancantar ya gaji kujerar Shugaba Kasa Muhammadu Buhari.
Mista Sylva ya mallaki fom din neman takarar a yayin da a ‘yan kwanakin nan ake fama da matsalar karancin man fetur musamman a wasu manyan birane na kasar ciki har da Abuja.
A kwanaki ukun da suka gabata, ‘yan Najeriya kan shafe sa’o’i suna bin layin shan man fetur a gidajen mai, matsalar da Kamfanin na NNPC ya jingina ga tafiyar hawainiya da ake yi wajen dauko dakon man fetur din daga daffonsa.