Ministan Tsaron Kasa na Isra’ila, Itamar Ben Gvir ya kai ziyara a masallacin Al-Aqsa, wuri mai tsarki da ke tsakiyar tashin hankali a gabashin Kudus.
Ministan ya kai ziyarar ce duk da barazanar da Hamas da Falasdinu suka yi tun can da farko kafin ziyarar.
- DAGA LARABA: Yadda Yaudara Ta Zamo Ruwan Dare A Fagen Soyayya
- Tirela ta murkushe sojoji 2, ta jikkata daya a Kwara
Ziyarar ministan mai tsatsaurar ra’ayi ta janyo martanin mai zafi na bangarorin gwamnatin Falasdinu da Hamas.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Falasdinu ta fitar da wata sanarwar yin Allah wadai da ziyarar a masallacin na Al-Aqsa, abin da ta kira da cewar tsokana ce.
Masallacin da ke a birnin Kudus na cikin yankin Falasdinu wanda Isra’ila ta mamaye tun a shekarar ta 1967.